Bamu Da Labarin Hukuncin Kotu Cewa Mu Kama Shugaban EFCC, Kakakin Yan Sanda

Bamu Da Labarin Hukuncin Kotu Cewa Mu Kama Shugaban EFCC, Kakakin Yan Sanda

  • Har yanzu, Da alamun hukumar yan sanda ba ta damke shugaban EFCC ba duk da umurnin kotu
  • Kakakin yan sandan Najeriya ya ce su dai ba su da masaniya game da wani umurnin kotu
  • Babbar kotun FCT ta umurci jefa shugaban EFCC kurkuku kan laifin raina mata hankali

Abuja - Hukumar yan sandan Najeriya ta bayyana cewa ba tada masaniya game da hukuncin kotu cewa ta kama Shugaban hukumar EFCC, AbdulRashin Bawa, kuma ta jefashi kurkuku.

Legit Hausa ta kawo muku rahoton cewa Alkalin kotu dake zamanta a Maitama Abuja ta kama Shugaban hukumar hana almundahana da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC) da laifi.

Alkalin kotun, Chizob Orji, ya kama Abdulrasheed Bawa da laifin saba umurnin da kotun tayi tun shekarun baya.

Saboda haka ya umurci hukumar yan sanda ta damke Abdulrasheed Bawa da gaggawa kuma a jefashi kurkukun Kuje har sai ya bi umurninsa.

EFCC/Police
Bamu Da Labarin Hukuncin Kotu Cewa Mu Kama Shugaban EFCC, Kakakin Yan Sanda Hoto: @OfficialEFCC
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Yace:

"Shugaban EFCC ya ki bin umurnin da wannan kotu tayi ranar 21 ga Nuwamba 2018 inda ta umurnin hukumar ta mayarwa wanda ya shigar da kara motarsa Range Rover (Super charge) da N40, 000,000.00 (Forty Million Naira)."
"Saboda saba wannan umurni na kotu, a jefashi kurkukun Kuje bisa raina hankalin kotu da saba umurnin da tayi ranar 21 ga Nuwamba 2018, har sai lokacin da ya bi umurnin."
"Sifeto Janar na yan sanda ya tabbatar da cewa an bi wannan umurni."

Alkali Chizoba ya yi watsi da bayanan da Francis Jirbo Lauyan EFCC, ya bayar kan rashin bin umurnin.

Martani kan hakan, Kakakin hukumar yan sanda, Olumiuywa Adejobi, ya bayyanawa Peoples Gazette:

"Ba ni da masaniyar wannan umurni. La'alla ba'a aike mana takardar ba."

Asali: Legit.ng

Online view pixel