An Fargabar Da Yawa Sun Mutu Yayin da Yan Bindiga Suka Bude Wuta a Shingen Yan Sanda
- Yan bindiga sun kai hari kan mutane a shingen binciken ababen hawa na 'yan sanda a jihar Anambra
- Bayanai sun ce ana fargabar mutane da dama sun rasa rayukansu sakamakon harin a yankin ƙaramar hukumar Ihiala
- Wani babban jami'i a hukumar 'yan sandan jihar ya tabbatar da lamarin, yace tuni kwamishina ya tura dakaru na musamman
Anambra - Mutane sun shiga tashin hankali biyo bayan wani kazamin hari da 'yan bindiga suka kai shingen binciken 'yan sanda a jihar Anambra.
Jaridar The Nation ta tattaro cewa ana fargabar mutane da yawa sun rasa rayukansu sakamakon harin yayin da wasu da dama suka jikkata.
Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 10:30 na safiyar nan a tsakankanin Titin Ihiala-Uli da ke yankin ƙaramar hukumar Ihiala a jihar Anambra.
An tattaro cewa lamarin ya tilastawa matafiya da sauran mutanen da ke kan hanyar gudun neman tsira domin 'yan bindigan sun cigaba da harbi ba ƙaƙƙauta wa.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Wane matakin jami'an tsaro suka ɗauka?
Bayanai sun nuna cewa jami'an tsaron da ke wurin sun tube Kakin dake jikinsu, kana suka ɗauki matsaya a dazukan dake kusa da gidajen yankin.
Tuni dai Motocin Bas na haya suka kauce wa bin hanyar Onitsha- Owerri a yanzu haka da muke kawo muku wannan rahoton saboda tsoron rasa rayuwarsu.
Jami'in hulɗa da jama'a na rundunar 'yan sandan jihar Anambra, Ikenga Tochukwu, ya ƙi ɗaga jerin kiran wayar da ake masa domin tabbatar da kai harin.
Amma wani babban jami'i a hukumar 'yan sandan jihar, wanda ya zanta da jaridar cikin kwarin guiwa, ya tabbatar da faruwar lamarin.
Yace, "Ban ji labarin rasa rai ko ɗaya ba amma zan iya tabbatar muku cewa lamarin ya shafi mutane yayin musayar wuta."
Majiyar ta ƙara da cewa kwamishinan 'yan sandan jihar Anambra, Echeng Echeng, ya tura tawagar dakaru na musamman zuwa Ihiala domin dakile lamarin, kamar yadda Dailypost ta ruwaito.
A wani labarin Rukunin shagunan 'yan sanda ya kama da Wuta da tsakar daren Talatan nan, miliyoyin Naira sun ƙone ƙurmus
Da misalin karfe 1:00 na daren wayewar garin yau Talata, wutar lantarki ta haddasa wata mummunar Gobara a Plazar 'yan sanda a Nasarawa.
Rahotannin da muka samu daga wani da abun ya faru a idonsa sun nuna cewa ba karamar asara 'yan kaauwa suka tafka ba a Gobarar.
Asali: Legit.ng