Birtaniya Ta Yi Ƙarin Haske Kan Shirin Ƴan Ta'adda Na Kai Hari Abuja, Ta Lissafa Jihohi 12 Da Ya Dace A Gujewa
- Ofishin jakandancin Birtaniya, kasashen rainon Birtaniya da cigaba, FCDO, ta sabunta shawarwari da ta bada ga tafiye-tafiye a Najeriya
- A sabbin shawarwarin da ta bada, FCDO ta ce bata bada shawarar yin tafiya zuwa Abuja, sai dai wanda ya zama wajibi
- Duk da hakan, FCDO ta gargadi cewa har yanzu akwai barazanar yiwuwar yan ta'ada su kai hari a Najeriya, kuma ta yi gargadin zuwa wasu jihohi
FCT, Abuja - Birtaniya a sabunta shawarwarin tafiye-tafiye da ta bawa yan kasarta a Najeriya, tana mai cewa kada a tafi Abuja sai dai kawai idan ya zama wajibi.
Ofishin jakandancin Birtaniya, kasashen rainon Birtaniya da cigaba wato FCDO ya bayyana hakan ne a shawarwarin tafiye-tafiye da ya wallafa a shafinsa a ranar Litinin 7 ga watan Nuwamba.
Karin Bayani: Gwamnatin Buhari Ta Sanar da Lokacin Cigaba da Sufurin Jirgin Kasa a Titin Kaduna-Abuja
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Legit.ng ta tunatar da cewa Birtaniya da Amurka sun yi gargadin babban harin "ta'addanci" a birnin tarayya Abuja, inda suka bukaci yan kasarsu su guji zuwa birnin idan ba ya zama dole ba.
Har yanzu akwai barazanar, in ji Birtaniya cikin sabuwar gargadi kan tafiye-tafiye
Duk da cewa mahukunta na Birtaniya sun ce yan kasar na iya zuwa Abuja, sunyi gargadin har yanzu akwai barazanar kai harin a birnin tarayyar.
Sanarwar ta ce:
"Yanzu FCDO bata bada shawarin yin tafiya zuwa birnin tarayya Abuja sai dai na wajibi, kuma har yanzu akwai barazanar, kuma an yi karin bayani kan barazanar kawo harin ta'addanci a yankin.
"Shawarar da FCDO ta bada na hana yin tafiya zuwa wasu wurare har yanzu yana nan."
Jihohin da aka shawarci yan Birtaniya kada su tafi
- Jihar Borno
- Jihar Yobe
- Jihar Adamawa
- Jihar Gombe
- Jihar Kaduna
- Jihar Katsina
- Jihar Zamfara
- Jihar Delta (yankunan ruwa)
- Jihar Bayelsa (yankunan ruwa)
- Jihar Rivers (yankunan ruwa)
- Jihar Akwa Ibom (yankunan ruwa)
- Jihar Cross Rivers (yankunan ruwa)
Jihohin da yan Birtaniya za su iya zuwa kawai don ayyuka masu muhimmanci
- Jihar Bauchi
- Jihar Kano
- Jihar Jigawa
- Jihar Neja
- Jihar Sokoto
- Jihar Kogi
- kilomita 20 na iyakokin Niger a Jihar Kebbi
- Jihar Abia
- yankunan da ba ruwa a jihohin Delta, Bayelsa da Rivers
- Jihar Plateau
- Jihar Taraba
Shawarar tafiye-tafiye: Akwai yiwuwar yan ta'adda za su kawo hari a Najeriya, in ji Birtaniya
Birtaniya, har yanzu ta ce akwai yiwuwar yan ta'adda su kawo hari a Najeriya, tana mai cewa barazanar ya karu a 2022.
Sanarwar ta kara da cewa:
"Mafi yawancin hare-haren da Boko Haram ko ISWA ke kaiwa na faruwa ne a jihohin Borno, Yobe da Adamawa a Arewa maso Gabas.
"Akwai kuma wasu hare-haren a wasu jihohi kamar Gombe, Kano, Kaduna, Plateau, Bauchi da Taraba.
"Barazanar kai harin a Najeriya ya hada da babban birnin tarayya, Abuja, da kewaye. Barazanar ya karu a 2022."
Bayan Amurka, Manyan Kasashen Duniya 3 Sun gano Yiwuwar kai hari a Birnin Abuja
Hukumomi a kasashen Kanada da Australiya sun gargadi mutanensu kan yin zuwa Najeriya saboda fargabar harin ta'addanci.
Wannan gargadin na zuwa ne a kimanin kwanaki uku bayan Amurka da Birtaniya sun ce sun gano barazanar rashin tsaro a kasar.
Asali: Legit.ng