‘Yan Bindiga Sun Hargitsa Kauye, Sun Yi Awon Gaba da Basarake da Mutanen Gari
- Miyagun ‘yan bindiga sun kuma aukawa wani kauye a karamar hukumar Zurmi da ke jihar Zamfara
- Ana maganar an yi awon gaba da Mai garin Kwangami, har zuwa yanzu ba a sake jin labarinsa ba
- Baya ga haka, ‘yan ta’addan sun dauke mutum 6 yayin da Bayin Allah da-dama ke jinyar raunuka
Zamfara - Rahoto ya zo cewa ‘yan ta’adda sun shiga karamar hukumar Zurmi a jihar Zamfara, sun kuma ci karensu babu babbaka.
Jaridar Punch tace wadannan mutane masu tada kayar baya sun yi nasarar dauke Mai garin wani kauye, Kwangami a jihar Zamfara.
Wani mazaunin yankin Zurmi mai suna Dahiru Amadu ya tabbatar da cewa ‘yan bindiga sun shigo masu dauke da manyan makamai.
A ranar Litinin dinnan ne miyagun ‘yan bindigan suka dauke har da Mai garin Kwangami, Mai martaba Muhammad Galadima.
An hada da mutane 6
Baya ga Alhaji Muhammad Galadima, an dauke wasu mutane shida da ake zargin an yi garkuwa da su ne domin a karbi kudin fansa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kamar yadda Dahiru Amadu ya fada da ya zanta da ‘yan jaridan, mazauna kauyen sun shiga halin lahaula a lokacin da aka kawo harin.
Bayan wadanda aka yi awon-gaba da su, mazaunin yace mutane da yawa sun samu rauni.
A cewarsa, an dauki Mai garin da sauran wadannan mutum shida ne a gidajensu, daga nan aka wuce da su zuwa sansanin ‘yan bindiga.
Babu zaman lafiya a Zurmi
“Yanzu haka mu na rayuwa cikin dar-dar domin ‘yan bindiga su na yawon kawo mana hari, su dauki mutane, su nemi kudin fansa.
Ba da dadewa ba ‘yan biniga suka dauke mana mutane 10 a gonakinsu, har yanzu su na hannunsu domin an gagara fanso su.”
- Dahiru Amadu
Rahoton yace ba a iya samun kakakin rundunar ‘yan sanda na jihar Zamfara, SP Mohammed Shehu domin jin ta bakinsa game da harin ba.
Ana samun sauki - NSA
An ji labari sababbin salon da sojoji da sauran dakarun tsaro suka dauka yana taimakawa wajen yakar ‘yan ta’adda da tsageru a Najeriya.
A wajen wani taro da Hukumar DIA ta shirya a Abuja, aka ji Mai ba Shugaban kasa shawara kan sha’anin tsaro, Babagana Munguno ya fadi haka.
Asali: Legit.ng