‘Yan Majalisa Sun Fadawa Buhari Masu Kawo Tasgaro Wajen Yakar Rashin Gaskiya

‘Yan Majalisa Sun Fadawa Buhari Masu Kawo Tasgaro Wajen Yakar Rashin Gaskiya

  • Kwamitin majalisa yana yin bincike a kan yadda aka zaftare kudi daga cikin kasafin Mai binciken kudi
  • An ware N2bn ayi ayyuka a ofishin babban mai binciken kudin gwamnati, daga baya kason ya koma N60m
  • Shugaban kwamitin binciken kudin gwamnati, Oluwole Oke yana ganin da hannun manyan jami’an kasar

Abuja - Kwamitin da ke binciken kudin asusun gwamnati ya yi ikirarin akwai wasu na kusa da shugaban Najeriya da ke cin dunduniyar gwamnatinsa.

A ranar Laraba, 2 ga watan Nuwamba 2022, Punch ta rahoto kwamitin yana cewa wadanda Muhammadu Buhari ya ba mukami sun zam masa cikas.

Shugaban kwamitin, Oluwole Oke yace wasu masu rike da mukamai a gwamnatin APC sun kawo ci-baya a yaki da rashin gaskiya da ake kokarin yi.

Honarabul Oluwole Oke ya bayyana cewa majalisar wakilan tarayya ba ta amince da rage kason kudin ayyuka na ofishin mai binciken kudi da aka yi ba.

Kara karanta wannan

Lauje cikin nadi: Majalisa ta gano ba a aikin wutar Mambila, tuni EFCC ta fara bincike

An rage abin da aka warewa babban mai binciken kudin gwamnatin tarayya wajen gudanar da ayyuka a kasafin kudin Najeriya daga N2bn zuwa N62m.

Wadanda ‘dan majalisar ya tuhuma da laifi sun hada har da Ministar tattalin arziki.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Taron FEC
‘Yan Majalisar FEC Hoto: @BashirAhmaad
Asali: Facebook

Rahoton yace Oke yana ganin laifin Ministar kudi, tsare-tsare da kasafin tattalin arziki, ofishin kasafin arzikin tarayya da Akawun gwamnatin tarayya.

Kwamitin ya kuma gayyaci jami’an da su hallara a gaban shi domin suyi masa karin bayani.

Lambar Folashade Yemi-Esan ya fito

Haka zalika shugaban kwamitin ya bukaci ganin shugabar ma’aikatan gwamnatin tarayya a gaban sauran abokan aikinsa a majalisa nan da mako daya.

Shugabar ma’aikatan gwamnatin tarayya, Folashade Yemi-Esan za ta wanke kanta daga zargin da ke kanta na kassara ofishin babban mai binciken kudi.

Za a canza shugaban INEC

A jiya Femi Adesina ya tabbatar da cewa Shugaban kasa bai da shirin canza Shugaban Hukumar INEC kafin zaben 2023 kamar yadda ake yadawa

Kara karanta wannan

Addu'a Muke Bukata Daga Amurka Ba Wai Su Tsorata Mu Ba, Ministan Buhari

Hadimin shugaban Najeriyan yace Muhammadu Buhari yana tare da Farfesa Mahmood Yakubu, kuma yana goyon bayan ayi aiki da BVAS a 2023.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng