Gwamna Bagudu Ya Baiwa Sabbin Kwamishinoni 9 da Ya Naɗa Wuraren Aiki

Gwamna Bagudu Ya Baiwa Sabbin Kwamishinoni 9 da Ya Naɗa Wuraren Aiki

  • Gwamna Atiku Bagudu ya tura sabbin Kwamishinoni Tara ma'aikatun da zasu yi aiki a gwamnatin jihar Kebbi
  • A wata sanarwa da aka raba wa manema labarai ranar Litinin, Gwamnan ya amince da tura mutanen ma'aikatu 10
  • Wannan na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan ya rantsar da sabbin Kwamishinonin da majalisa ta amince da su

Kebbi - Gwamnan jihar Kebbi, Abubakar Atiku Bagudu, ya amince da tura sabbin kwamishinoni Tara da ya naɗa kwanakin baya zuwa ma'aikatun da zasu yi aiki a gwamnatinsa.

Tura kwamishinonin zuwa wuraren aiki na kunshe ne a wata sanarwa da aka fitar ranar Litinin mai ɗauke da sa hannun Sakataren gwamnatin jihar, Babale Umar Yauri.

Gwamna Atiku Bagudu na jihar Kebbi.
Gwamna Bagudu Ya Baiwa Sabbin Kwamishinoni 9 da Ya Naɗa Wuraren Aiki Hoto: dailytrust
Asali: Facebook

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa sanarwar, wacce aka raba wa manema labarai a Birnin Kebbi, ta bayyana ma'aikatar da kowane ɗaya daga cikin Kwamishinonin zai yi aiki.

Kara karanta wannan

Yadda Naga Matata Tana Saduwa da Ɗan Uwana, Miji Ya Faɗa Wa Kotu Komai, Ya Nemi Raba Auren

Yadda gwamnan ya ba kowa ma'aikata

A cewar Sanarwan, Ibrahim Augie, zai jagoranci ma'aikatar kuɗi, Abubakar Chika Ladan zai karɓi ma'aikatar ayyuka da Sufuri, Abdullahi Muhammad Magoro, an tura shi ma'aikatar yaɗa labarai da Al'adu kuma shi ne zai kula da ma'aikatar tattara bayanai da sadarwa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sauran sun haɗa da, Hassan Muhammad Shalla, wanda aka tura ma'aikatar ilimin matakin farko da na Sakandire, yayin da Aminu Garba Dandiga, zai jagoranci harkokin ma'aikatar dabbobi da kiwon kifi.

Haka nan kuma, Dr. Abba Sani Kalgo, ya samu ma'aikatar kasafi da cigaban tattalin arziki, Jafar Muhammad, ma'aikatar lafiya yayin da Mamuda M. Wara, zai tafi ma'aikatar ƙasa da gidaje.

Sai kuuma na ƙarshe, Hayatu A. Bawa, wanda zai karɓi ragamar ma'aikatar muhalli kuma sanarwan ta ƙara da cewa sabbin Kwamishinonin zasu shiga Ofis ne nan take.

Gwamnan Gombe ya yi garambawul a gwamnatinsa

Kara karanta wannan

Rudani yayin da Gwamna El-Rufai ya yafewa wasu fursunoni hudu saboda wani dalili

A wani labarin kuma Gwamnan Gombe Ya Nada Sabbin Kwamishinoni da Hadimai, Ya Yi Garambawul

Gwamna Inuwa Yahaya na jihar Gombe ya naɗa sabbin kwamishinoni biyu da mashawarta na musamman.

Yayin rantsar da su, gwamnan ya yi garambawul a majalisar zartaswans kana ya baiwa sabbin wuraren da zasu yi aiki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel