Budurwa Ta Cancarawa Saurayinta Aski, Ta Ba da Mamaki a Wani Bidiyo

Budurwa Ta Cancarawa Saurayinta Aski, Ta Ba da Mamaki a Wani Bidiyo

  • Wani matashi dan Najeriya ya jawo cece-kuce a shafin sada zumunta yayin da ya nuna irin kyakkyawan askin da budurwarsa ta yi masa
  • A cewarsa, abu ne mai kyau gaye ya samu budurwar dake sana'ar gyaran gashi, domin hakan zai taimaka matuka
  • Jama'a a kafar sada zumunta sun yi martani, sun ce dole ya biya kudin aski tunda shine sana'ar budurwar tasa

Wani matashi dan Najeriya ya jawo cece-kuce a kafar sada zumunta yayin da ya yada bidiyon wata budurwarsa gwana kuma kwararriya a sana'ar aski.

A bidiyon da ya yada a TikTok, matashin ya nuna kalan askin da budurwar tasa ta zauna ta cancara masa, lamarin da yasa mutane da dama luguden lebe.

Matashin da budurwarsa ta yi masa aski
Budurwa ta cancarawa saurayinta aski, ta ba da mamaki a wani bidiyo | Hoto: TikTok/@its_x_and_p
Asali: UGC

Matashin ya kuma bayyana cewa, budurwar tasa duk da a wurin sana'arta ta yi masa askin, bai biya ko kobo ba, masu karatu ai soyayya ta fi kudi ko?

Kara karanta wannan

Ministan farko na sufurin jiragen sama a Najeriya, babban mai kare Nnamdi Kanu ya rasu

A bidiyon lokacin da take masa askin, budurwar bata nuna wani damuwa ba, kuma bata ce uffan ba, kawai dai an ga tana aikinta na aski ne cikin kwarewa.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Jama'ar TikTok dai sun ki hakura, sai da suka tofa albarkacin bakinsu, kuma mun tattaro muku kadan daga martanin jama'a.

Kafin nan, kalli bidiyon a nan:

Martanin jama'a

Tessy yace:

"Dan uwa karya kake, kudin da za ka biya zai zama ninki 2 ne."

Tolani yace:

"Idan da Legas ne wannan budurwar tai min aski to tabbas ta kware."

shooladamilola tace:

"Lol, nima sana'ar aski nake, saurayina na biyan ninki biyu ne o."

user7635242586691 yace:

"Wannan shine ka nemi budurwa mai aski kenan."

Oluwah_Sheyi yace:

"Ta yaya ba zan karbi kudi ba tunda nima ba kyauta na koya ba."

Kara karanta wannan

Bidiyo: Matashiya Yar Shekaru 40 Ta Koka Saboda Rashin Mijin Aure, Ta Roki Allah Ya Kawo Mata Agaji

Wani Dan Najeriya Ya Fasa Asusun da Ya Yi, Ya Kirga Tsabar Kudi N5.5m a Cikin Wani Bidiyo

A wani labarin, wani dan Najeriya ya shajja'a jama'a da dama a kafar TikTok yayin da cikin alfahari ya nuna kudin da ya tara a asusu da suka kai N5,000,000.

A wani bidiyon da ya yada a shafinsa mai suna @offwhite633, an ga lokacin da ya ciro katuwar akwatin da ya yi wannan asusu, kana ya fasa ta cikin tsanaki.

Mabiyansa a kafar TikTok sun shiga mamakin ganin yadda ya tara makudan kudade 'yan N1000 a cikin akwati kamar wannan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel