Yanzu-yanzu: An Tare Babban Titin Legas, Ana Tsoron An yi Garkuwa da Bayin Allah
- Akwai alamu masu karfi da ke nuna an yi garkuwa da wasu matafiya da yammacin yau a garin Legas
- An samu motoci a hanyar Legas zuwa Ibadan a bude a kan titi, ana tunanin an yi gaba da mutanen cikinsu
- Wani wanda ya ci karo da motocin dazu yana zargin garkuwa da mutanen aka yi, ba fashi da makami ba
Lagos - Mutanen da zuwa yanzu ba a san adadinsu ba, sun fada hannun masu garkuwa da mutane a hanyar Legas zuwa garin Ibadan.
Daily Trust ta kawo rahoto a yammacin Juma’a, 28 ga watan Oktoba 2022 cewa an tare motoci a a titin Legas zuwa Ibadan an dauki mutane.
Ana zargin masu garkuwa da mutane ne suka yi wannan danyen aiki dazu. Hakan ya jawo matafiyan da ke bin wannan hanya suka rude.
A dalilin abin da ya faru, mutane da yawa sun hakura da tafiyarsu, sun fasa bin hanyar, wasu sun saki hannu a titin, sun bi layi na dabam.
Ba a san mutum nawa aka dauka ba
Rahoton yace wannan abin ya faru ne a daidai jami’ar addini ta Dominion da ke KM 24 a kan babban titin na Legas zuwa Ibadan da ke Legas.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Wani wanda ya shaida abin da ya auku, ya fadawa manema labarai, babu wanda zai iya cewa ga adadin mutanen da aka yi awon gaba da su.
Wannan mutumi ya tabbatar da cewa an tare motoci uku, an dauke mutanen da ke cikinsu. Daga cikin motocin ya ga Jeep da Toyota Camry.
"Na ga motoci uku da kofofinsu a wangale, babu ko mutum daya da aka gani a cikinsu, kuma babu alamar wurin aka shiga da su.
Da farko mun yi tunanin fashi da makami ne, amma ba haka ba ne. Da za mu ga wadanda aka yi wa fashi, ban ga kowa ba da na isa.”
- Wanda ya ga lamarin
Da aka tuntubi shugaban dakarun Amotekun na shiyyar Legas, Olayinka Olayanju ya shaidawa jaridar cewa bai san da labarin garkuwa da mutanen ba.
Haka zalika rundunar ‘yan sanda ta jihar ba ta ce komai a game da batun ba har zuwa yanzu.
'Yan ta'adda za su kai hare-hare
Dazu kun ji labari cewa wasu kasashen Turai da na Amurka suna cigaba da biyewa USA da Birtaniya a kan barazanar tsaron da ‘Yan Najeriya ke fuskanta.
Hujjoji na kara bayyana ga kasashen Duniyan cewa lallai ‘Yan ta’adda sun yi tanadin kai wa mutane hari a garuruwa fiye da 20, daga ciki har da birnin Abuja.
Asali: Legit.ng