Bidiyon Yadda Magidanci Ya Mayar Da Kauyensa Ya Zama Birni, Ya Gina Hanyoyi Da Hannunsa
- Wani matashi mai shekaru 46 ya inganta rayuwar mutane da dama a kauyensa ta hanyar gina masu hanyoyi
- Mutumin mai suna Faustin Kimaro ya shafe tsawon shekaru 20 yana aikin gina hanyoyi ba tare da wani ya saka shi ba
- A cewarsa, Allah ya sa mashi wani tunani da ya karfafa masa gwiwar yin aiki duk da suka da rashin karrama shi
Wani mutumin Bukoni a yankin kudancin Tanzania ya sha ruwan yabo kan sauya kauyensa da yayi inda ya gina hanyoyi shi kadai ba tare da taimakon kowa ba.
Mutumin wanda ke da yara biyu mai suna Faustin Kimaro ya gina hanyoyin ne ta hanyar amfani da kayan gida kamar su fatanya da diga.
Afrimax ta ziyarci mutumin mai shekaru 46 a mahaifarsa sannan ta yada wani bidiyo da ke nuna wasu hanyoyi da ya gina.
Kimaro ya fara aikin tun yana da shekaru 17
Mutumin wanda ya rasa matarsa a wani mummunan hatsarin mota a 2006 ya fada ma Afrimax cewa ya fara aikin yana da shekaru 17 kuma yana aikin hakar hanyar kullun.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Ya ce garin na fama da rashin hanyoyi tun 1994 sannan matafiya na bi kananan jeji ne don tafiya.
Amma abun da yasa shi fara hakar shine wani tunani da yayi ikirarin Allah ya saka mashi.
"Wata rana Allah ya saka mun wani tunani. Ya kasance hasashe inda nake iya hango wani a kauyen nan yana rashin lafiya amma ya ki zuwa asibiti. Har nayi tunanin idan mai shi zai iya mutuwa a nan, me zai faru?
"Sai na dauki fatanyata sannan na fara gina hanya," in ji shi.
Ya ce wasu mutane sun caccake shi, cewa babu wata lada da zai samu a wannan aiki da yake yi ba, amma sai Kimaro bai nuna damuwa ba. Kimaro ya ce babu wanda ya taba biyansa ko sisin kwabo.
"Na yi hakan ne saboda mutane masu mota kuma basu bani ladan komai ba. Suna ganin yakamata nayi hakan ne..."
Kimaro ya kuma yi amfani da duwatsu da kasa wajen daidaita hanyoyin.
Kalli bidiyon a kasa:
Jama'a sun yi martani
Angela Jackman ta ce:
"Allah ya ci gaba da baka karfin zuciya da damar ci gaba da aikin alkhairin da kake yi."
Inez Sangare ya ce:
"Mutane na zaton komai kudi ne tunani zai kawo maka arziki eh kalli yadda mutumin nan yayi tunanin hanya don kowa shi mutum ne mai daraja."
Cecil Samuel ya ce:
"Mutumin kirki Allah ya albarkace ka sannan ya kareka a kodayaushe, ina fatan cewa mutane za su fara taimaka masa da iyalinsa da kudi."
Ta Rabu Da shi Saboda Tayi Sabon Saurayi: Magidanci Ya Ruguza Gidajen Da Ya Ginawa Matarsa Da Surukarsa
A wani labarin kuma, wani mutumin kasar Malawi mai suna Francis Banda wanda ke zaune a yankin Ntcheu ya hau kanen labarai bayan ya rushe gidaje biyu a kokarinsa na daukar fansar yaudararsa da aka yi.
Malawi 24 ta rahoto cewa matar Banda ta rabu da shi kwanan nan don kasancewa da wani daban, lamarin da ya kona masa rai har ya kai ga ruguza gidajen da ya gina mata da surukarsa.
A bisa ga wani faifan murya da ya saki, ya bayyana cewa sun shafe tsawon shekaru 13 da matarsa kuma har sun haifi yara uku.
Asali: Legit.ng