Wata Mata Ta Daba Wa Magidanci Wuka Har Lahira Yayin da Fada Ya Hada Su

Wata Mata Ta Daba Wa Magidanci Wuka Har Lahira Yayin da Fada Ya Hada Su

  • Wata mata mai suna Gift a takaice ta yi ajalin wani mutumi ta hanyar daɓa masa wani abu har yace ga garin ku nan
  • Wani bidiyo da ya karaɗe kafafen sada zumunta ya nuna matar a cikin mota an sanya mata Ankwa yayin da take amsa laifinta
  • A bayananta ta ce faɗa ya kaure a tsakaninsu ne lokacin da mamacin ya kamata a cikin wani gida tare da wani mutumi na daban

Delta - Wata mata yar asalin jihar Delta da aka bayyana sunanta da Gift a takaice ta daɓa wa wani mutumi da har yanzu ba'a gano bayanansa ba wuƙa har lahira yayin da faɗa da kaure a tsakaninsu.

A wani Biduyo da ya watsu a kafafen sada zumunta, an hangi Gift da sarƙar jami'an tsaro zaune a cikin mota, inda ta amsa laifinta yayin da ake mata tambayoyi.

Kara karanta wannan

Wata Budurwa Na Neman Saurayi Mara Ko Sisi, Tace Masu Kudi Suna Da Girman Kai, Hotunanta Sun Ja Hankali

Rikicin mace da namiji.
Wata Mata Ta Daba Wa Magidanci Wuka Har Lahira Yayin da Fada Ya Hada Su Hoto: punchng
Asali: UGC

Ta kuma yi ikirarin cewa faɗa ya kaure tsakaninsu ne lokacin da mamacin ya kamata da wani a gidan na biyun, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

A bayananta, Girf ta ce:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Ya zo nema na a gidan wani mutumi na daban kuma ya kama ni dumu-dumi tare da wannan mutumin. Nan take saɓani ya shiga tsakanin mu muka kaure da faɗa bayan ya ganni da mutumin."

Meyasa matra ta yi ajalin mutumin?

Yayin da aka tambayeta menene dalilin da ya hasalata har ta yi ajalin mutumin, Gift ta ƙara da cewa, "Kawai ya zo ne ya gana da ni da farko."

Bugu da ƙari, a Bidiyon dake yawo a kafafen sada zumunta, matar tace ita 'yar asalin jihar Delta ce amma tana zaune a garin Uwoghwa.

A wani labarin na daban kuma Wani Mutumi Ya Kaɗu Bayan Ya Laɓe Ya Ji Tattaunawar Matarsa da Kawarta a Waya, Bidiyo Ya Ja Hankali

Kara karanta wannan

Bidiyon Saurayi Ya Kaiwa Budurwa Ziyara a Kauye, Yayi Mata Wanki da Diban Ruwa

Wata mai juna biyu ta shiga ban ɗaki a gidan aurenta domin tattauna wa da kawarta kan Mijinta da kuma maza.

A kalaman da ta yi da kawarta ta wayar salula, matar tace ba ta cire wa kowa hula ba baki ɗaya maza makaryata ne har da Mijinta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel