Nnamdi Kanu Ya Shigar da Karar Gwamnatin Buhari, Yana Neman a Biya Shi N100bn
- Ganin gwamnatin tarayya ta ki kyale shi ya samu ‘yanci, Nnamdi Kanu ya shigar da sabuwar kara
- Kanu yana ganin tsare shi da ake yi alhali kotu tace a fito da shi, ya sabawa tsarin mulki da doka
- Shugaban na IPOB yayi karar DSS da AGF, yana so a ci tarar kudi N100bn a hannun gwamnati
Abuja - Jagoran kungiyar Indigenous People of Biafra, (IPOB), Nnamdi Kanu ya shigar da kara a gaban Alkali, yana neman diyyar Naira biliyan 100.
Vanguard ta kawo rahoto a ranar Laraba, 27 ga watan Oktoba 2022 cewa Nnamdi Kanu yana karar gwamnatin Najeriya kan tsare shi da DSS ke yi.
A karar da Kanu ya shigar a babban kotun tarayya mai zama a garin Abuja, ya roki Alkali ya yi umarni ga hukumar DSS tayi maza-maza ta sake shi.
Baya ga haka, shugaban kungiyar ta IPOB yana neman Naira biliyan 100 bisa zargin ci masa zarafi da rashin mutuntasa a matsayinsa na ‘Dan Adam.
Kanu yake cewa ya zama dole ya shigar ne domin gwamnatin Najeriya ta ki bin umarnin kotun daukaka kara, tana cigaba da garkame shi har gobe.
Jaridar The Cable tace Mike Ozekhome, SAN shi ne asalin Lauyan da ya tsayawa Kanu.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Za a bukaci AGF, DSS a kotu
An shigar da karar mai lamba FHC/ABJ/CS/1945/2022 tun a ranar 21 ga watan Oktoba. AGF, DSS da Shugaban DSS suna cikin wadanda ake tuhuma.
A takardar shari’ar, ana so kotu tace rike Kanu da ake yi tun daga 13 ga watan Oktoba, bai halatta ba, ya saba doka, babu dalili, zalunci ne kuma taka doka ne.
“Wannan ya sabawa hakkina na Bil Adama da damar ‘dan kasa na yin zirga-zirga kamar yadda yake a sashe na 34, 35, 36, 39 da 41 na tsarin mulkin 1999.
- Nnamdi Kanu
Wani roko da ke gaban kotu shi ne ta hana hukuma keta alfarmar Kanu nan gaba ta hanyar taka dokar Najeriya da kundin tsarin mulki na shekarar 1999.
Rahoton yace a karshe wanda ake tuguma yana so Alkali ya ci gwamnati tarar Naira biliyan 100.
Akwai hadari zuwa Najeriya
An samu rahoto a makon nan, Gwamnatocin kasashen Australiya da Kanada sun fadawa mutanensu su guji tafiya zuwa Najeriya, idan ba ta zama dole ba.
Kasashen Australliya da Kanada sun yi gargadi cewa tafiya zuwa kasar Afrikan a yanzu tana da hadari sosai ta fuskar tsaro, har a babban birnin tarayya.
Asali: Legit.ng