Zaben 2023: Jerin Jihohin Najeriya 6 Da Suka Fi Yawan Masu Kada Kuri'a Ya Fito

Zaben 2023: Jerin Jihohin Najeriya 6 Da Suka Fi Yawan Masu Kada Kuri'a Ya Fito

  • Hukumar zabe mai zaman kanta INEC ta bayyana jerin jihohin da suka fi yawan masu rajistan zabe
  • Gabanin babban zaben shekarar 2023, hukumar zaben na kasa ta bayyana cewa Legas, Kano, Kaduna, Rivers, Katsina da Oyo ne a kan gaba
  • Karin nazari da hukumar ta yi ya nuna yankin arewa maso yamma ne ke kan gaba wurin yawan mutane da suka yi rajista don zaben 2023

A ranar Laraba, 26 ga watan Oktoba, shugaban hukumar zabe na kasa, INEC, Farfesa Mahmood Yakubu, ya sanar da cewa adadin wadanda suka yi rajistan zabe ya kai miliyan 95.5.

Nazarin farko da aka yi game da sunayen wadanda suka yi rajistan ya nuna cewa Legas, Kano, Kaduna, Rivers, Katsina da Oyo ne a kan gaba wurin yawan masu rajistan zabe, The Punch ta rahoto.

Kara karanta wannan

2023: Kashi 40 Na Mutanen Da Suka Yi Sabuwar Rijistar Zabe Dalibai Ne, INEC

Shugaban INEC
Zaben 2023: Jerin Jihohin Najeriya 6 Da Suka Fi Yawan Masu Kada Kuri'a Ya Fito
Asali: Original

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Jihohin da suka fi yawan mutane masu rajistan zabe

Nazari ya nuna cewa:

1. Legas na da kashi 7.57 cikin 100

2. Kano, kashi 6.35 cikin 100

3. Kaduna, kashi 4.65 cikin 100

4. Ribas, kashi 3.77 cikin 100

5. Katsina, kashi 3.76 cikin 100 kuma

6. Oyo na kashi 3.76 cikin 100

Legit.ng ta lura cewa masu zaben a jihohi shida sun kai miliyan 27.68 ko kashi 29.49 na dukkan masu rajistan zaben.

A cewar akalluman masu zaben na farko, jihohin Legas, Kano, Kaduna da Ribas na kan gaba da masu zabe 7,075,192; 5,927,565; 4,345,469 da 3,532,990, kamar yadda aka jero su.

Masu biye musu sune Katsina da 3,519,260 da Oyo da ke da 3,275,045.

Har yanzu Legas ta rike matsayinta na jiha mafi yawan masu zabe, ta samu kari daga miliyan 6.5 zuwa miliyan 7.07.

Kara karanta wannan

Jihohi 6 Mafiya Yawan Masu PVC Bayan INEC Ta Cire Sunan Mutum Miliyan 2.7

Kano ma ta samu karin sabbin masu rajistan zabe 469,818, hakan yasa yanzu tana da masu zabe miliyan 5.9.

Kaduna na da masu zabe miliyan 4.3 yayin da Ribas ta sha gaban Katsina ta zama na hudu a yawan masu rajistan zabe.

Zaben 2023: Peter Obi Ya Ce Ko Ƴaƴan Cikinsa Ba Su Yarda Da Shi Idan Ya Yi Alƙawari, Mutane Sun Yi Martani

Peter Obi, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar LP, yana shan suka a soshiyal midiya saboda amsar da ya bada kan tambayar da aka masa game da yadda zai farfado da lantarki a Najeriya.

Mai gabatar da shirye-shirye a gidan talabijin na Arise TV ya ce wannan shine dalilin da yasa ya kamata dan takarar LP din ya fitar da manufofinsa ga kasar a rubuce don mutane su gani su yi nazari.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164