Rikicin Ganduje da Rarara: Alan Waka Yace Kare Mutuncin Dauda Ya Fi Kamfen Din Takararsa A 2023
- Gabannin zaben 2023, ana ci gaba da samun takun saka tsakanin bangeren Gwamna Abdullahi Ganduje da mawaki Dauda Kahutu Rarara
- Aminu Alan Waka ya sako baki cikin lamarin a wannan karon inda yake goyon bayan Rarara
- Alan Waka wanda ke neman kujerar dan majalisar tarayya a jihar Kano ya ce yakin kare mutuncin Dauda ya fi yakin neman kujerar da yake yi
Kano - Alaka na kara tsami tsakanin shahararren mawakin siyasa, Dauda Kahutu Rarara da gwamnatin jihar Kano karkashin Abdullahi Umar Ganduje.
Sai dai a wannan karon, shahararren mawaki kuma mai neman takarar kujerar dan majalisa a Kano karkashin jam’iyyar ADP, Aminu Alan Waka ya saka baki a rikicin.
Alan Waka wanda ya nuna goyon bayansa ga abokin sana’arsa, ya ce kare mutuncin Dauda ya fi masa yakin neman zaben kujerar da yake yi a 2023.
Mawakin ya ce takararsa fansa ce a wajen kare hakki da mutuncin Rarara.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Alan waka wanda ya bayyana hakan a shafinsa na Instagram, ya ce:
“Yaƙin kare mutuncin Dauda ya fi yaƙin neman zaɓen ɗan takarar ɗan Majalisar tarayya agareni.
“Mu yi mutunci da mutuncinka, ka yi mutunci da mutuncinmu shi ne babban arziƙi na zaman tare.
“Takarata fansa ce a wajen kare mutunci da Hakkin DAUDA.”
A baya dai mawaki Rarara na cikin yan hannun damar Ganduje da gwamnatinsa inda yana kan gaba wajen mara masa baya a 2015 da 2019.
Sai dai kuma, gabannin zaben 2023, mawakin baya goyon bayan dan takarar jam’iyyar APC, Dr Nasiru Yusuf Gawuna, ya nuna goyon baya ne ga Sha'aban Ibrahim Sharada na Action Democratic Party, ADP.
Ana haka ne Rarara ya yi wata sabuwar waka inda ya soki Ganduje tare da kiransa da Hankaka mai fuska biyu. Ya kuma zarge shi da dakile sunansa a cikin kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na Bola Tinubu.
Sai gashi sabbin bayanai sun fito cewa gwamnatin Kano ta ce gidan Rarara da ke jihar an gina ta ne a kan magudanar ruwa.
Abokan sana'arsu sun yi martani
Legit.ng ta tattaro wasu daga cikin martanin jama'a a kasa:
realabmaishadda ya ce:
"Wannan GASKIYA DAN HALAK ❤️❤️❤️."
rashidamaisaa ta ce:
"@ala gaskiya mutum nagari sanin halacci sai dan halak kuma wanda yagaji arziki wllh haka zasu ganshi haka kuma zasubarshi ko iya farantawa marshi dayake addu’ar su ta isa wllh kairan in sha allah."
ayshatulhumairah ta rubuta:
"Allah ya taimaki Sarki ."
ishaq_abdul_ ya ce:
"Bama goyon bayan cin mutuncin manya, idan ya gyara Allah zai taimake shi."
khalifa__man ya ce:
"Kuna ruwa kuwa domin kun taba wanda baa tabawa yanxu gashi zaman kano ya gagareshi ."
An Yi Watsi Da Sunan Rarara a Kwamitin Kamfen Din Tinubu
Mun ji a baya cewa jam’iyyar APC ta saki sabbin sunaye na mambobin kwamitin yakin neman zaben dan takararta na shugaban kasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, bayan ta yi yan gyare-gyare a wanda ta fitar a baya.
Har yanzu shugaban hukumar tace fina-finai ta jihar Kano, Isma'ila Na'abba Afakalla na nan a matsayin mataimakin darakta a bangaren masu nishadantarwa na kwamitin kuma zai jagorancin yankin arewa maso yamma.
Jarumi Nuhu Abdullahi na nan a matsayinsa na mataimakin mai kula da jin dadin kwamitin yan wasan. Sani Idris Moda ma yana nan a cikin kwamitin.
Asali: Legit.ng