Jami’ar Jihar Ribas Ta Haramtawa Dalibai Sanya Dangalallen ‘Siket’, Sarkar Kafa, Da ‘Tattoo’

Jami’ar Jihar Ribas Ta Haramtawa Dalibai Sanya Dangalallen ‘Siket’, Sarkar Kafa, Da ‘Tattoo’

  • Jami'ar jihar Ribas ta haramtawa dalibai maza da mata shigar rashin kamun kai a harabar makaranta
  • Wata sanarwa da jami'ar ta fitar ta bayyana abubuwan da aka ce kada a sake ganin dalibai suna yi a cikin makaranta
  • Ana yawan samun lokuta da ake kai ruwa da rana da dalibai kan irin shigar da suke a makaranta, musamman mata

Jihar Ribas - Hukumar gudanarwar jami'ar jihar Ribas ta haramtawa dalibai mata sanya dangalallen fatari, sarkar kafa da sanya girar bogi da dai sauran shigan rashin kamun kai.

Gudanarwar makarantar ta kuma haramtawa dalibai shiga makaranta da zanen jiki da aka fi sani da 'tattoo' a kokarin jami'ar na rage yaduwar badala a harabarta.

Wannan na fitowa ne daga wata sanarwar da magatakardar jami'ar, Dr. S. C. Enyindah ya fitar a ranar 19 ga watan Oktoba, SaharaReporters ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: INEC ta ware jihohi 3 da za su yi zaben gwamnan 2023 a wani lokaci daban

Jami'a a kudancin Najeriya ta haramta shigar rashin da'a
Jami’ar Jihar Ribas Ta Haramtawa Dalibai Sanya Dangalallen ‘Skirt’, Sarkar Kafa, Da ‘Tattoo’ | Hoto: saharareporters.com
Asali: UGC

Sanarwar ta bayyana cewa, an sanya wannan haramci ne ga dalibai bayan dogon zama da tsanaki tsakanin hukumomi da manyan jiga-jigan tafiyar da harkokin jami'ar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jami'ar ta bayyana cewa, ta samar da dokar hanin ne a zamanta na ranar 29 ga watan Satumban 2022.

Abubuwan da aka haramtawa dalibai

Wani yankin sanarwar na cewa:

"Ta wannan haramcin, yanzu ya haramta ga kowane dalibi ya yi shiga kamar haka a harabar makaranta:
1. Sanya riga mai geza-geza ga dalibai mata.
2. Sanya gajeren fatari da bai kai gwiwa ba ga dalibai mata.
"3. Yiwa gashi fenti ga dalibai maza da mata.
4. Sanya burgujejen wando ga dalibai maza da mata.
5. Sanya 'yan kunne ga dalibai maza da kuma sanya dan kunne a hanci ga dalibai mata.
"6. Yin zanen jiki ga dukkan dalibai maza da mata.

Kara karanta wannan

Yajin ASUU: Jihar Kwara ta shirya tallafawa daliban jami'a da wani tukuici mai kyau

7. Sanya sarkar kafa ga dalibai mata. 8. Sanya dogon gashin ido ga dalibai mata. 9. Sanya rigar da ke nuna cibiya ko mama ga dalibai mata.
"10. Sanya fasasshen wando ga dalibai maza da mata.
11. Sanya silifan wanka ko gajeren wandon bacci zuwa aji."

Ba wannan ne karon farko da ake samun irin wannan doka a jihohin Kudancin Najeriya, gwamnatin jihar Anambra ta kawo irin wannan doka a makarantun sakandare.

Manyan Yan Kasuwan Arewa, Kungiyar Malamai Kano, Manyan Tijjaniyya da Kadiriyya Sun Bayyana Goyon Bayan Tinubu

A wani labarin, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC, Bola Ahmad Tinubu ya sake samun karbuwa a idon manyan jiga-jigan yankin Arewacin Najeriya, musamman Kano.

Jiga-jigan masu fada a ji a Arewacin Najeriya da suka hada da 'yan kasuwa da malamai sun bayyana goyon bayansu ga dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC.

Kara karanta wannan

Hadimin Buhari Ya Caccaki Peter Obi Kan Kaiwa Dubban Jama’a Tallafin Sunki 24 na Biredi

A jihar Kano, shugabannin 'yan kasuwa, malamai, 'yan Tijjaniya, Ahlus Sunnah da 'yan Kadiriyyah ne suka bayyana goyon bayansu gareshi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel