Yadda Gwamnan PDP Ya Rabawa Jihohi 5 Gudumuwar Naira Biliyan 2 a Shekara 1
- Abin da Nyesom Wike ya bada a matsayin kyauta ko kuma tallafi daga bara zuwa yanzu ya zarce N2bn
- Gwamnan ya kashewa jihohin Sokoto, Kaduna da Legas Naira biliyan 2.1 a shekara da ‘yan watanni
- Nyesom Wike ya yi rabon kudi har a Arewacin Najeriya a lokacin da musiba ta aukawa mazauna yankin
Port Harcourt, Rivers – Mai girma Gwamna Nyesom Wike mai mulkin jihar Ribas ya saba taimakawa jihohi da daidaikun mutane da-dama da tallafin kudi.
Mun fahimci a watanni 15 da suka wuce, gwamnan na Ribas ya bada gudumuwar Naira biliyan 2.1 ga jihohin da bukata ta taso masu a fadin kasar nan.
Punch ta bi yadda gwamnan ya raba gudumuwa daga watan Junairun 2021 zuwa Oktoban nan.
1. Jihar Sokoto
A lokacin da gobara ta ci babbar kasuwar Sokoto, Gwamnan Ribas ya tallafawa Gwamna Aminu Tambuwal da kyautar N500m a ranar 10 ga Junairun 2021.
Gwamna Atiku Bagudu mai makwabtaka da Sokoto, ya ba ‘yan kasuwar gudumuwar N30m a lokacin.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
2. Jihar Akwa Ibom
Nyesom Wike ya bada kyautar N600m ga jihar Akwa Ibom a Mayun 2021. Gwamnan ya bada kudi wajen gina asibitin koyar da likitoci da ke Awa a garin Onna.
3. Jihar Bayelsa
Kokarin gwamnan bai tsaya nan ba, ya bada N500m domin a gina jami’ar aikin likitanci a garin Yenagoa. An yi wannan a watan Fubrairun shekarar nan.
4. Jihar Kaduna
Da Gwamnan ya zo Kaduna domin yakin neman zama ‘dan takaran PDP a 2023, ya bada gudumuwar N200m domin kula da wadanda rikicin ‘yan bindiga ya ci.
5. Jihar Legas
A makon jiya Nyesom Wike ya ziyarci Legas, nan ma ya raba N300m ga matan jami’an gwamnatin Legas, yace ya yi hakan domin yabawa ayyukan da ake yi.
Lissafin LP a zaben 2023
Kun ji labari takarar Peter Obi a zaben sabon shugaban kasa tana cigaba da motsa siyasa, musamman ganin yadda Obi ya samu karbuwa a Kudancin Najeriya.
Ana hasashen Jam’iyyar Labour Party za ta gwagwiyi kuri’un da Atiku Abubakar ya samu a 2019. Wannan tasiri zai iya aiki har a wasu jihohin da ke Arewa.
Asali: Legit.ng