Manyan Hanyoyi 3 Da Hauhawar Farashin Gas Ɗin Girki Zai Shafi Ƴan Najeriya
Yan Najeriya na fama da kallubale da dama da suka hada da matsin tattalin arziki da hauhawar farashin kayayyaki. Daga cikin abin tada hankalin shine hauhawar farashin iskar gas (LPG) da ake girki da shi wanda ya shafi masu gida da kasuwanci tun bara.
Alkalluma daga Hukumar Kididdiga Ta Najeriya, NBS, ta bayyana cewa a duk shekara, farashin gas ya karu da kashi 60.69 cikin 100 daga N6,164.97 a Satumban 2021 zuwa Satumban 2022.
Hauhawar farashin gas da raguwar karfin sayayyar abubuwa ga daidaikun mutane ya kara nauyin wahalhalu ga yan kasa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kimanin mako daya bayan hukumar samar da gas ta Najeriya, NLNG, ta ayyana tsayar da samar da gas, masu saye sun fara kokawa kan yiwuwar karuwar farashin gas a Abuja da kewaye.
Misali, Mrs Onyeka Odoh, mazauniyar Bwari a Abuja ta fada wa Daily Trust cewa ta siya kilogram 12 na gas kan N10,500, an samu karin N700 cikin sati daya kacal.
Karin ya shafi yan Najeriya a manyan hanyoyi uku kamar haka:
1. Karin farashin abincin sayarwa
Yawan karin farashin gas na girki ya janyo wuraren sayar da abinci da dama su kara kudin abinci ko rage yawan abincin da suka sayarwa kwastomomi.
Masu sayar da abinci da gidajen sayar da abinci sun dade suna fama da tsadar kayan abinci da gas. Hakan yasa wasu suka rage adadin abinci, wasu kuma suka kara kudin abincinsu.
2. Nemo wasu hanyoyin girki
Mutane masu girki a gidaje da wuraren siyar da abinci sun fara neman wasu hanyoyin girki misali amfani da itace, gawayi ko dussan kafintoci don kauracewa siyan gas saboda tsadarsa.
Tunda farashin wadannan abubuwan ba s kai gas ba kuma suna iya biyan bukata, al'umma na kara bukatarsu musaman gawayi da itace.
3. Matsalolin lafiya masu alaka da girki da gawayi da itace
Abubuwan da mutane suka koma amfani da su a madadin gas din girki suna da illolin su. Misali itace na gurbata muhalli kuma yana tsananta canjin yanayi, kuma suna da illoli ga lafiyar masu amfani da su.
Duk da cewa Najeriya ta rattaba hannu kan yarjejeniyar sauyin yanayi ta 2017, kasar na fama da kallubalen mata da yara suna fama da matsalar yawan amfani da itace da gawayi.
Cibiyar Kasa Da Kasa Ta Makamashi, Muhalli Da Cigaba, ICEED, ta ce yan Najeriya 93,000 ke mutuwa duk shekara saboda hayaki da suke shaka daga girki da itace, kuma ya fi shafar mata da yara.
Hakan na nufin a kalla mata yan Najeriya 450,000 za su mutu sakamakon girki da itace ko gawayi a shekara biyar idan ba su samu wani hanyar girbi mai sauki ba wanda ba shi da hatsari ga lafiyarsu.
Tsadar rayuwa: Jihohin da suka fi ko'ina tsadar gas din girki a Najeriya
Hukumar kididdiga ta kasa ta ce matsakaicin farashin da ake cika tukunyar gas din girki na 5kg ya karu zuwa 3,921.35 a watan Mayun 2022.
Hakan na kunshe ne a cikin rahoton farashin gas na watan Mayun 2022 da hukumar NBS ta saki a shafinta na Twitter.
Asali: Legit.ng