Mai Kula da Shago ta Fusata Yayin da Mai Sayen Kaya Yazo da Jaka Makare da 'Yan N10

Mai Kula da Shago ta Fusata Yayin da Mai Sayen Kaya Yazo da Jaka Makare da 'Yan N10

  • Wani dan Najeriya ya kawo rudani mai zafi a shagon siyayya yayin da yazo gaban mai shago da jaka makare da kudi
  • Ochulo, ya yada bidiyon lokacin da ya je shago da 'yan Naira goma-goma da biyar-biyar kana ya nemi mai shago ta kirga
  • Bidiyon abin da ya faru ya jawo cece-kuce da mamaki a kafar TikTok, jama'a da dama sun yi martani

Ochulo, wanda aka fi sani da Odogwu Ten Five ya yada wani bidiyon yadda ya je shagon siyan kayan alatu domin sayen wani abun.

Sai dai, kudaden da ya bayar a shagon siyayyan sun jawo rikici tsakaninsa da budurwa mai kula da shagon, wacce ta shiga mamakin ganinsa da irin kudin.

Mutumin da ya je siyan kaya da 'yan N10 fal jaka
Mai Kula da Shago ta Fusata Yayin da Mai Sayen Kaya Yazo da Jaka Makare da 'Yan N10 | Hoto: TikTok/@chulo_wayz.
Asali: UGC

A gajeren bidiyon da ya yada, an ga lokacin Ochulo ya bude jakarsa makare da 'yan Naira goma-goma sannan ya nemi budurwar da ta kirga su.

Kara karanta wannan

Tashin hankali yayin daka tsige DPO daga kujerarsa bisa zargin kashe dan bindiga

Martanin budurwa mai shago

Yayin da Ochulo ya gama ciro kudaden daga jaka, budurwar sai ta tsaya cak tana kallonsa cikin rudani tare da ta'ajibin me yake so. Ta tambaye shi nawa ne dama a cikin jakar.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Duk da haka, ya dage dole sai dai ta girka kudin da kanta tukuna, amma dai hakan zai bata mata lokaci da yawa.

Kalli bidiyon:

Martanin jama'a

Jama'a da dama a kafar sada zumunta sun tofa albarkacin bakinsu. Ga kadan daga ciki:

@perfect dc yace:

"Za ta kirga kuwa har sai ta gaji."

@darrin_G yce:

"Jumillar kudin ba lallai ya kai 2k ba."

@Drunk Psychologist yace:

"Ke da wa zaku kirga wannan kudin."

@Goldenrumen yace:

"Injin kirge zai kama da wuta yau kenan."

@user45703995289 yace:

"Ina son wannan bidiyon, ina matukar girmama kudadenmu. Kai, kalli yadda naira 10 ta fi Dala, Fam & Yuro kyau."

Kara karanta wannan

Har da cire riga: Bidiyon mutumin da ya birkita zaman lafiyan banki saboda an taba kudinsa

@damonny1 yace:

"Matar fa da rude."

@242_D_great yace:

"Kawai ki yi amfani da na'urar buga lissafi tunda a dauri suke."

@HIGHEXbillion1 yace:

"Dole kuwa ta kirga."

Mutane 3 da Aka Gano Ba Su da Laifi Bayan Shafe Shekaru a Gidan Yari

A wani labarin, akwai labarai da yawa da ake bayar wa na mutanen da aka ayyana ba su da laifi bayan shafe shekaru a magarkama da sunan suna da laifi.

Wani mai shekaru 51, Eddie Bolden, ya kwashi garabasar biliyoyi bayan da ya shafe shekaru 22 a gidan yari bisa kuskure.

Legit.ng ta tattaro labarin wasu mutane uku da wannan iftila'i na yaddda 'shari'a sabanin hankali' ya afka dasu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel