Amurka da Burtaniya Sun Gargadi 'Ya'yansu Dake Najeriya Su Kula, Za a Iya Kai Hari Abuja

Amurka da Burtaniya Sun Gargadi 'Ya'yansu Dake Najeriya Su Kula, Za a Iya Kai Hari Abuja

  • Gwamnatin Amurka da ta Burtaniya sun gargadi 'ya'yansu mazauna Najeriya da su kula matuka kan yiwuwar samun hare-hare
  • Gwamnatocin sun kuma ba jama'arsu shawarin yadda za su kula da kansu daga hare-haren ta'addanci a Najeriya
  • Babban birnin tarayya Abuja bai tsira daga hare-haren da 'yan ta'adda ke kaiwa ba, duk kuwa da nan ne tushen mulkin Najeriya

Abuja - Gwamnatin Amurka da Burtaniya sun gargadi 'ya'yan kasashensu mazauna Najeriya da su kula, akwai yiwuwar samun hare-hare a Najeriya, musamman a babban birnin tarayya Abuja.

Wannan na fitowa ne daga sashen ba da shawari kan tsaro na ofishin jakadancin Amurka dake Najeriya, Premium Times ta ruwaito.

Amurka da Burtaniya sun ce akwai yiwuwar kai hare-hare a Abuja
Amurka da Burtaniya Sun Gargadi 'Ya'yansu Dake Najeriya Su Kula, Za a Iya Kai Hari Abuja | Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Ofishin ya kuma bayyana cewa, hare-haren ka iya aukuwa ne a gine-ginen gwamnati, wuraren ibada, makarantu, kasuwanni da shagunan siyayya, otal, mashawa, gidajen cin abinci da na wasanni har kan jami'an tsaro da sauransu.

Kara karanta wannan

Rundunar Yan Sanda Ta Magantu Kan Yuwuwar Kai Harin Ta'addanci a Najeriya

A bangare guda, ofishin na Amurka ya ce, 'yan kasashen waje mazauna Najeriya da sauran kungiyoyin kasa da kasa ba za su tsira daga hare-haren ba.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Saboda haka ne, ofishin jakadancin na Amurka yace, zai rage ayyukan yau da kullum saboda gujewa fadawa hadari.

Bugu da kari, ofishin ya ba Amurkawa mazauna Najeriya shawarin su yi waiwaye ga daburn tsaro da kare kai, su kasance da wayoyinsu da caji don jiran ko ta kwana kuma su rike katin shaida.

Burtaniya ta bi sahun Amurka

Bata sauya zane ba, ofishin jakadancin Burtaniya a Najeriya ya bi sahun Amurka wajen ba da wannan gargadi.

A cewar ofishin:

"Akwai karin barazanar harin ta'addanci a Abuja. Ya kamata ku kasance a ankare, kuke zirga-zirga cikin tsanaki, kuke bibiyan kafafen yada labaran cikin gida da kuma shawarin hukumomin tsaro."

Kara karanta wannan

Tashin hankali yayin daka tsige DPO daga kujerarsa bisa zargin kashe dan bindiga

Dukkan wadannan ofisoshi biyu na kasashe mabambanta sun bayyana sanarwarsu ne ta saharsu ta yanar gizo.

Akalla mako guda kenan da gwamantin Australlia ta shawarci 'yan kasar da su guji tafiya zuwa kasar ta Najeriya saboda barazanar tsaro.

Yan Sanda Sun Kama Kwamandan IPOB/ESN, Sun Lalata Sansanonin Horar da Tsageru a Ebonyi

A wani labarin, 'yan sandan jihar Ebonyi sun yi nasarar kame wasu mambobin kungiyar nan ta ta'addanci IPOB da sojojinta ESN bayan wani samamen da ta kai kan wasu sansanonin horar da tsageru.

'Yan sandan sun bayyana cewa, wadannan sansanoni na tsageru suna cikin wani duhun daji ne na kauyen Omege a lardin Agba ta karamar hukumar Ishielu ta jihar, The Cable ta ruwaito.

Chris Anyanwu, kakakin rundunar 'yan sandan jihar, ya kuma bayyana cewa, jami'ai sun kwato makamai da alburusai da kakin sojoji da dai sauran kayayyakin aikata laifi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.