Abin da Ya Sa Na Yarda Na Amsa Lambar Girman da Shugaban kasa Ya Ba Ni – Fasto
- Ignatius Ayau Kaigama bai karbi shawarar da mutane suka ba shi da aka ce za a ba shi lambar OFR ba
- Akwai wadanda suka hurowa Limamin Katolikan wuta ya watsawa gwamnatin tarayya kasa a idanu
- Faston ya soki wannan gurguwar shawara, ya karbi lambar OFR daga hannun Muhammadu Buhari
Abuja - Babban limamin Katolika a birnin Abuja, Ignatius Ayau Kaigama yace an huro masa wuta sosai domin ya ki karbar lambar girman gwamnatin Najeriya.
Daily Trust ta rahoto Rabaren Ignatius Ayau Kaigama a ranar Asabar, 22 ga watan Oktoba, 2022, yana bayanin abin da ya sa ya ki watsi da lambar girmamawan.
Ignatius Ayau Kaigama yana cikin mutanen da aka zaba domin a karrama a shekarar nan, amma mutane suka ba sa shawarar ka da ya amince da wannan shaida.
A wani jawabi da ya fitar a garin Abuja, Ayau Kaigama yace ya yi mamaki da ya ji labarin sunansa yana cikin wadanda Muhammadu Buhari zai karrama a 2022.
A cewarsa, mutane sun yi ta aiko masa da sakon taya murna, amma kuma wasu ‘yan daidaiku su ka ba shi shawarar ka da ya amince ya karbi wannan lambar girma.
Rahoton yace a karshe ba haka aka yi ba, Iyau Kaigama ya karbi lambar girma na OFR.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jawabin Ignatius Ayau Kaigama
“Wani ya yi magana a shafin sada zumunta kafin in karbi lambar girman, ‘Me zai sa Bishof ya karbi kyautar a kasar da ake fama da yunwa, rashin tsaro da kashe-kashe; Wa zai fadawa gwamnati gaskiya kenan?’
Bayan na karbi lambar girman, wani ya ke cewa: ‘Da ka ki karbar wannan ko da cikin ruwan sanyi ne, da ba ka nuna cewa lallai kana tare da al’umma ba?’”
- Ignatius Ayau Kaigama
Ignatius Kaigama bai ga hikimarsu ba
Babban faston yake cewa yadda dauki lamarin shi ne idan har bai karbi lambar girmamawan ba, tamkar ya nesanta kan shi ne da kokarin gyara Najeriya da ake yi.
Daily Post tace malamin addinin bai ga hikimar watsi da karramawar da aka yi masa ba, saboda ana fama da kashe-kashe da rashin abubuwan more rayuwa.
Ayau Kaigama yace idan ba za a karbi lambar girman ba, to za ayi watsi da kundin kasafin kudin Najeriya da shugaba Muhammadu Buhari ya gabatar a majalisa.
...Chimamanda Ngozi Adichie ta ki karba
Kuna da labari mashahuriyar marubuciyar Duniya, Misis Chimamanda Ngozi Adichie ba ta karbi lambar girmamawa daga hannun gwamnatin Najeriya ba.
Chimamanda Ngozi Adichie tayi watsi da lambar girman da aka shirya za a ba ta tare da wasu 'yan kasa, tayi hakan ne salin-alin ba tare da fito tayi magana ba.
Asali: Legit.ng