ICPC Ta Rufe Sansanin NYSC da Makarantu 62 Da Ake Yin Digirin Bogi a Najeriya

ICPC Ta Rufe Sansanin NYSC da Makarantu 62 Da Ake Yin Digirin Bogi a Najeriya

  • Hukumar ICPC mai yaki da rashin gaskiya da makamantan laifuffuka tace tana kokarin tsabtace harkar ilmi
  • Shugaban ICPC a Najeriya, Farfesa Bolaji Owasanoye yace sun rufe makarantu masu bada takardar digirin bogi
  • Farfesa Bolaji Owasanoye ya yi wannan jawabi wajen wani taro da aka shiryawa daliban manyan makarantu

Abuja - Hukumar ICPC mai yakar cin hanci da rashawa da sauran makamantan laifuffuka tayi nasarar rufe makarantun bogi fiye da 60 a kasar nan.

Vanguard ta rahoto shugaban hukumar ICPC na kasa, Farfesa Bolaji Owasanoye yana cewa ana samun shaidar digiri na karya a wadannan makarantu.

A yunkurin gyara harkar ilmi, baya ga makarantu, shugaban na ICPC yace sun rufe wani sansani sukutum na bogi na masu yin hidimar kasa (NYSC).

Farfesa Bolaji Owasanoye ya yi wannan bayani a wani taro da aka shiryawa dalibai domin yakar rashin gaskiya a makarantu na gaba da sakandare.

Kara karanta wannan

Saura Wata 7 a Bar Ofis, Buhari Ya Fadawa Ministoci Su Fara Shirye-Shiryen Mika Mulki

Hukumar dillacin labarai na kasa watau NAN tace hukumar ICPC ta shirya taron ne ga daliban wasu zababbun makarantu da ke birnin tarayya Abuja.

Hannatu Mohammed ta wakilci Shugaban ICPC

Hannatu Mohammed ta wakilci Farfesa Owasanoye a wajen taron. Mohammed ce mai wakiltar matasa a majalisar da ke sa ido a kan aikin hukumar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaban ICPC
Shugaban ICPC, Farfesa Bolaji Owasanoye Hoto: www.channelstv.com
Asali: UGC

A jawabin da aka gabatar a madadinsa, Sun ta rahoto Farfesan yace babu wata kasa a Duniyar nan da za ta iya cigaba fiye da matakin ilmin al’ummarta.

Farfesan yake cewa an kafa kungiyoyin yaki da rashin gaskiya a makarantu domin dalibai su taka rawarsu wajen yakar rashin gaskiya a matsayinsu.

Dalibai za su bada gudumuwarsu

“Wadannan kungiyoyi za su taimakawa dalibai su zama suna yakar rashin gaskiya a ko ina, kuma su canza tunanin sauran abokan karatunsu.

Kara karanta wannan

Kamfen 2023: Ba a yi nisa ba, INEC ta fara kuka da yadda jam'iyyun siyasa ke kare jini biri jini

Kungiyoyin za kuma su taimakawa dalibai su ba shugabanni gudumuwarsu a makarantu da-dma wajen rage rashin gaskiya a bangaren ilmi.”

Owasanoye yace barnar da ake yi a makarantu sun hada da cin hanci da rashawa, lalata da dalibai, satar amsar jarrabawa, badakalar kwangiloli da satar kudi.

Haka zalika ana saidawa dalibai kayan karatu, ko a bada takardar shaidar karatu na bogi ko biyan kudi domin samun gurbin yin karatu a manyan makarantun.

Zage-zage a Twitter

An samu labari tsohuwar Ministar Najeriya da sauran mutane sun yi Allah-wadai da zagin da Shugabar Nigerian Commission tayi a shafinta na sada zumunta.

Kafin Abike Dabiri-Erewa tayi zagin, wani mutumi ne ya zo shafinta na Twitter ya fara ci mata mutunci, ita kuwa tace ba za a raina mata wayau haka kurum ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel