Saura Wata 7 a Bar Ofis, Buhari Ya Fadawa Ministoci Su Fara Shirye-Shiryen Mika Mulki
- Muhammadu Buhari ya bukaci Ministoci su fara tattara bayanan da ake bukata wajen canjin gwamnati
- A karshen watan Mayun 2023 wa’adin Muhammadu Buhari zai cika, za a nada sabon shugaba a Najeriya
- Shugaban kasar yana so a tanadi bayanan manufofi da tsare-tsaren gwamnatinsa da cigaban da aka samu
Abuja - Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya umarci Sakataren gwamnatin tarayya ya cigaba da aikin lura da kokarin da Ministocinsa suke yi.
Mai girma shugaban kasar yace abin da Boss Mustapha zai yi, zai taimaka wajen tattara rahotannin da za ayi amfani da su a wajen canjin gwamnati.
Daily Trust tace a halin yanzu saura watanni bakwai da ‘yan kwanaki wa’adin gwamnati mai-ci ta shude, amma ana maganar mika ragamar mulki.
Muhammadu Buhari ya bada wannan umarni a zaman karshe da aka yi a ranar Talata wajen taron da aka shiryawa Ministocin tarayya a birnin Abuja.
Ana wannan taro ne domin duba ayyukan da Ministocin suke yi, sannan a kara masu haske.
Shugaban kasa ya hada SGF da aiki
Buhari ya bukaci duk wani Minista da Sakataren din-din-din na tarayya ya tabbatar da cewa rahoton duka ayyukan da suke yi yana zuwa ofishin SGF.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Duk bayan watanni uku, ana bukatar Minista ya kawo cigaban da aka samu a ma’aikatarsa, da wannan za a san ko gwamnati tana ci wa manufofinta.
Rahoton yace shugaban Najeriyan ya bukaci a gabatar masa da bayani a kan aikin Ministocinsa.
An ja-kunnen Ministocin tarayya
Bugu da kari, Mai girma Buhari ya ja-kunnen Ministoci da Sakatarorin din-din-din cewa ka da suyi wasa da aiki, domin ba zai yarda da saba alkawari ba.
Duk da zabe ya gabato, shugaban kasar ba zai amince da wannan a matsayin uzuri ba, yace dole ne Ministoci su dage a kan asalin ayyukan da ke gabansu.
Buhari yace burinsa shi ne a fito da yadda za a damka mulki ga sabon gwamnati dauke da bayanin manufofin da tsare-tsaren gwamnati da inda aka kwana.
Dalilin Gwamnoni na bin Tinubu
A baya an samu rahoto cewa Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya yi bayanin dalilin Gwamnonin Arewa na bin bayan Asiwaju Bola Tinubu a zaben 2023.
Malam Nasir El-Rufai yace za su marawa Bola Tinubu baya ya zama shugaban kasa saboda hakan ne adalci tun da 'Yan Arewa sun yi shekaru takwas a mulki.
Asali: Legit.ng