‘Dan Takaran Jam’iyyar NNPP ya Raba Kayan Tallafin Ga Wadanda Masifa ta Auka Masu
- Omatseye Nesiama ya taimaka da kayan bada tallafi ga wadanda ruwa ya yi masu gyara a yankin Neja-Delta
- ‘Dan takaran Sanatan na Kudancin jihar Delta ya yi rabon kayayyakin ne a kananan hukumomin Isoko
- Mummunar ambaliyar ruwan saman da aka yi a shekarar nan ya shafi wasu garuruwan da ke jihar Delta
Delta - ‘Dan takaran Sanatan kudancin jihar Delta a karkashin jam’iyyar NNPP, Omatseye Nesiama ya ziyarci wuraren da aka yi ambaliya a jihar Delta.
Jaridar Punch tace Commodore Omatseye Nesiama (retd.) ya kai ziyara zuwa garuruwan Igbide da Ofagbe da ke karkashin karamar hukumar Isoko.
Mutanen wadannan yankuna sun gamu da mummunan ambaliya sakamakon ruwan sama mai karfi.
Baya ga ziyarar Allah ya kyauta, Omatseye Nesiama wanda yake neman zama Sanata a zaben 2023, ya raba kayan tallafi domin tausaya wadanda abin ya shafa.
Baba-Ahmed Ya Gargadi Yan Najeriya Akan Su Guje Wa Yan Takara Masu Nuna Kabilanci da Addini a Zaben 2023
Rahoton yace kayayyakin da aka raba sun hada abinci kamar su doya, sinkin burodi, buhunan gari, shinkafa, gishiri, sukari, taliya, man gyada sai kayan miya.
Har ila yau ‘dan takaran ya raba biscuits, sabulan wanka da na wanki da sauran kayan ban-daki.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Jama'a suna cikin mawuyacin hali
Hakan ya faru ne a sanadiyyar ambaliyar da aka yi wanda ta ci makaratar firamaren Ebe a garin Ovrode da gidajen masu bautar kasa watau NYSC da ke Isoko.
Da yake jawabi, Nesiama ya yi kira ga ‘yan siyasa da masu hali su ajiye bambancin ra’ayi a gefe guda, su taimakawa mutanen da suka shiga mawuyacin hali.
‘Dan takaran ‘dan majalisa na mazabar Isoko ta Arewa, Dr. Daniel Uroghome ya yi kira ga gwamnatocin tarayya da na jiha da su kawowa yankin na sa agaji.
Shugaban jam’iyyar NNPP na jihar Delta, Cif Friday Efetobor ya ji dadin yadda aka raba kayan tallafin, ya yi kira ga sauran ‘yan takara a 2023 suyi koyi da shi.
Wasu daga cikin wadanda aka taimaka sun godewa gudumuwar da Nesiama ya kawowa al’umma.
Gidan gwamnati zai iya nutsewa
An ji labari Gwamna Douye Diri yace Bayelsa ta shiga mawuyacin hali a sanadiyyar ambaliyar ruwan sama, hakan ya sa aka kira taron majalisar tsaro na gaggawa.
Douye Diri ya yi bayanin yadda karatu suka tsaya, tituna suka gutsure. Gwamnan yayi kira ga gwamnatin tarayya ta sa dokar ta-baci domin a magance lamarin.
Asali: Legit.ng