Jerin Jami’o’i 10 Mafi Nagarta da Za Ku Iya Karanta Ilimin Likitanci a Najeriya

Jerin Jami’o’i 10 Mafi Nagarta da Za Ku Iya Karanta Ilimin Likitanci a Najeriya

Jami'ar Ibadan (UI) da jami'ar Legas (UNILAG) ne a saman jerin jami'o'i mafi nagarta a Najeriya, inda dalibai za su iya karanta ilimin likitanci da sanin ilimin lafiyar hakora a cewar rahoton jerin jami'o'in duniya.

The Times Higher Education (THE), mujallar da ke tattara nagartattun jami'o'i a duniya ta fitar jerin manyan jami'o'i na 2023, kuma UI da UNLILAG sun fito a tsakanin na 401 zuwa 500 a jerin jami'o'in duniya.

Jami'ar Bayero dake Kano kuwa, ta fito a tsakanin na 1001 zuwa 1200 a jerin jami'on duniya baki daya, kuma itace ta uku a nagartattun jami'o'in Najeriya.

Jami'o'in da za ku iya zuwa domin karanta ilimin likitanci a Najeriya
Jerin jami'o'i 10 mafi nagarta da za ku iya karanta ilimin likitanci a Najeriya | Hoto: AMINU ABUBAKAR/AFP
Asali: Getty Images

Mujallar dake tattara wannan rahoto dai a kasar Burtaniya take, kuma tana duba kyawun jami'o'i ne a fadin duniya.

Kara karanta wannan

BUK da wasu manyan jami'o'in Najeriya 9 da kowa zai iya karanta ilimin shari'a

Ana duba jami'o'in ne ta fannin kokari, nagarta da dai sauransu. Abubuwan da ake mai da hankali wajen zakulo jami'o'in sun hada da karantarwa, bincike, tasirin ilimi da kuma karbuwa a idon duniya.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Jerin jami'o'i 10 mafi nagarta a fannin ilimin likitanci da lafiyar hakora

A kasa mun tattaro muku jerin jami'o'in da suka fi nagarta wajen karantar da ilimin likitanci a Najeriya:

LambaJami'o'in NajeriyaMatsayi a NajeriyaMatsai a Duniya
1Jami'ar Ibadan (UI)1401-500
2Jami'ar Legas (UNILAG)1401-500
3Jami'ar Bayero ta Kano (BUK)31001-1200
4Jami'ar Benin (UNIBEN)41201-1500
5Jami'ar Ilorin (UNILORIN)41201-1500
6Jami'ar Najeriya ta Nsukka (UNN)41201-1500
7Jami'ar Obafemi Awolowo (OAU)41201-1500
8Jami'ar Fasaha ta Ladoke Akintola (LAUTECH)81501+
9Jami'ar Nnamdi Azikiwe (UNIZIK)81501+
10Jami'ar Tarayya ta Alex Ekwueme, Ndufu-Alike10"Akwai bayani"

Kara karanta wannan

Usman Rimi: Ɗalibin Likitanci Na Ajin Karshe Wanda Ya Fara Sana'ar Dafa Abinci Saboda Yajin Aikin ASUU Ya Rasu A Sokoto

Tambihi: Jami'ar Tarayya ta Alex Ekwueme dake Ndufu Alike basu samu lambar matsayi ba, duk da kasancewarta cikin jami'o'i 526 da suka ba da bayanansu don tantance su.

Jami'ar ta gabatar da takardun tantance jami'a, amma bata cika ka'idojin da ake bukata ba. Sai dai, ta amince a bayyana ta a jerin jami'o'in da ake da rahotonsu a hannu.

Gwamnatin Buhari Ta Bankado Makarantun Bogi 349 Dake Cin Gajiyar Shirin Ciyar da Dalbai a Nasarawa

A wani labarin kuma, a karkashin shirin ciyar da 'yan makaranta na gwamnatin tarayya, an gano akalla makarantun bogi 349 a jihar Nasarawa dake cin gajiyar wannan shiri da aka yi don makarantun firamaren gwamnati.

Wannan batu na gano badakala na kunshe a cikin wani rahoton jaridar The Nation, kamar yadda Legit.ng Hausa ta tattaro.

Rahoton ya bayyana cewa, kudaden da gwamnati ta ware don ciyar da dalibai a wadannan makarantu da babu su sun fada aljihun wasu mahandama, inji kwamitin ma'aikatar jin kai karkashin Mallam Abdullahi Usman.

Kara karanta wannan

Rikicin PDP: Wike Ya Dauki Ortom, Makinde Da Ikpeazu Sun Shilla Kasar Waje, An Bayyana Dalilin Fitarsu

Asali: Legit.ng

Online view pixel