Manta da Elon Musk, Ga Labarin Mansa Musa, Basaraken Afrika da ya Ninka Musk Arziki

Manta da Elon Musk, Ga Labarin Mansa Musa, Basaraken Afrika da ya Ninka Musk Arziki

  • Yayin da Elon Musk ya kasance mutum mafi arziki a duniya a yau, masana tarihi sun ce kudinsa ba komai ba bane idan aka hada shi da Mansa Musa
  • Mansa Musa basarake ne ‘Dan Afrika wanda yayi rayuwa a karni na 14 kuma masana tarihi sun ce shi ne mutumin da yafi kowa kudi a tarihin duniya
  • Sai dai duk da wannan kudin, ba komai ne Mansa ya samu ba domin akwai lokacin da ya bayar da buhun zinari aka bashi buhun gishiri daya tak

Kamar yadda bayanin Bloomberg ya bayyana, manyan masu kudin duniya sune Elon Musk, Bernard Arnault, Jeff Bezos da Gautam Adani

Rahoton ya nuna cewa Elon Muska yana da tarin dukiya da ta kai $198 biliyan. Duk da kuwa wannan yawan dukiyar, Musk bai zo ko kusa da Mansa Musa ba, basaraken Afrika da yayi rayuwa a karni na 14 wanda ke da dukiya ta bada mamaki.

Kara karanta wannan

Buba Galadima: Mutum 440 Cikin Wadanda Buhari Ya Ba Wa Lambar Yabo Ya Kamata Suna Gidan Yari

Mansa Musa
Manta da Elon Musk, Ga Labarin Mansa Musa, Basaraken Afrika da ya Ninka Musk Arziki. Hoto daga @MansaMusa

A takaice, Musk baya cikin biloniyoyin duniya idan muka duba tarihi, Scmp sun yi ikirarin cewa John D. Rockefeller da Augustus Caesar sun fi shi kudi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Waye Mansa Musa?

A Mandinka, Mansa na nufin basarake ko shugaba.

Kamar yadda BBC ta bayyana, an haifa Musa Keita wuraren 1280CE yayin sarautar Keita.

An haife shi a gidan sarauta da suka karba karagar mulki a 1312 C3 yayin da ‘dan uwansa Mansa Abu-Bakr yayi watsi da karagar domin wata tafiya a teku.

Ko a lokacin da ya hau kan karagar mulkin, an tabbatar da cewa yana da mashahuriyar dukiya.

Masana tarihi sun ce masarautar Mali a wannan lokacin ita ce inda aka fi samun gwal a duniya kuma take samarwa da samar wa da rabin duniya kamar yadda gidan tarihin birtaniya ya bayyana.

Kara karanta wannan

Buhari Ya Amince a Raba Buhunan Kayan Abinci 240, 000 a Wuraren da Aka Yi Ambaliya

Ya kudin Mansa Musa suke?

Wasu masu kiyasi sun kwatanta azikinkinsa da $400 biliyan zuwa $500 biliyan duk da akwai matukar wahala a yi kiyasin daidai duba da lokacin ana amfani da gwal, gishiri da filaye ne wurin bayyana arziki.

Masana tarihi masu tarin yawa sun sakankance cewa arzikinsa yafi duk yadda wani mahaluki zai iya kintatawa.

Ranar da ya bayyana arzikinsa a duniya

A matsayinsa na Musulmi, Musa ya fara tafiya zuwa Makka daga 1324 zuwa 1325 wanda yanzu aka ce shi ne tafiya mafi almubazzaranci da wani mahaluki yayi a duniya kamar yadda Magnates Media suka bayyana.

Musa ya tashi da nufin bayyanawa duniya sunansa, kuma tafiyar nan ta nisan kilomita 6,500 ita ce damar da zai yi hakan.

BBC ta rahoto cewa basaraken ya bar kasar Mali da mutane 60,000 wadanda suka hada da mata da maza, daga dogarai zuwa matukan rakuma da bayi dauke da jakunkunan danyen gwal.

Kara karanta wannan

Yan Sanda Sun Gayyaci Mutum 5 Kan Mutumin Da Ake Rufe Tsirara Na Fiye Da Shekaru 20 A Kaduna

Musa da tawagarsa sun ratsa ta hamadar Sahara da Misra inda suka isa Cairo inda basaraken ya dinga rabon gwalgwalai.

Ya raba zinari mai yawa ta yadda ya rikirkita tattalin arzikin kasan wanda hakan yasa suka fada matsalar hauhawar farashin kayayyaki na tsawon shekaru 10 bayan tafiyarsa.

Wasu daga cikin nasarorin da Musa ya samu

Musa ya mayar da hankali wurin farfado da biranen dake masarautarsa. A gaskiya yayi kokari don har yanzu akwai alamun kokarin da yayi.

Ya gina makarantu, dakunan karatu da masallatai kuma ya taimaka wurin mayar da Timbuktu zama cibiyar al’ada da ilimi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng