EFCC: ‘Dan Damfara Ya Rasa Dukiyarsa Har Abada, Ya Sallama Kudi, Bitcoin na N40m

EFCC: ‘Dan Damfara Ya Rasa Dukiyarsa Har Abada, Ya Sallama Kudi, Bitcoin na N40m

An gama sauraron shari’ar da ake yi tsakanin Alkali Tanimu da kuma lauyoyin hukumar EFCC

Ana zargin Alkali Tanimu wanda aka fi sani da Yahoo Boy da mallakar dukiya ta hanyar damfara

Alkali ya bada umarnin karbe wasu kudi da dukiyoyin Yahoo Boy, a mallakawa gwamnatin tarayya

Lagos - A ranar Juma’ar da ta gabata, Alkalin babban kotun tarayya da ke zama a garin Legas ya bada umarnin karbe dukiyar Alkali Tanimu.

Rahoton da ya fito da The Nation ya bayyana cewa kotu tace a karbe 1.982, 022, 84 na kudin yanar gizo na Bitcoin da aka samu wajen Alkali Tanimu.

Kamar yadda aka kawo rahoto, darajar kudin yanar gizon ya kai N40m. Sannan gwamnati ta karbe wayoyin iPhone masu tsada da kudi a bankuna.

Wayoyin wannan mutum da ake yi wa lakabi da Yahoo Boy da kotu tace a karbe, a damkawa gwamnati su ne iPhone 12 Pro Max sai iPhone 7.

Kara karanta wannan

Wani Gwamna Ya Umurci Dalibai Da Ma’aikatan Gwamnatin Jiharsa Su Fara Sanya Kayan Gargajiya Ranar Juma’a

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Alkali ya gamsu da karar EFCC

Mai shari’a Nicholas Oweibo ya zartar da wannan hukunci bayan sauraron korafin Lauyan da ya tsayawa hukumar EFCC, Sulaiman I. Sulaiman.

Sulaiman I. Sulaiman ya kafa hujja da sashe na 17 na dokar hana satar kudi da makamantan laifuffuka da sashe na 44(2) na kundin tsarin mulki.

EFCC.
Hedikwatar EFCC Hoto: dailynigerian.com
Asali: UGC

Lauyan yace an yi amfani da wayoyin Yahoo Boy wajen gudanar da bincike na musamman.

Da ya gama sauraron bayanin da Lauyan ya aiko gabansa, mai shari’a Oweibo yace ya gamsu a karbe dukiyoyin, a sallamawa gwamnatin tarayya.

Ana zargin Yahoo Boy ya mallaki makudan kudi, Bitcoins da wayoyin zamanin ne ta hanyoyin da suka sabawa oka, don haka aka nemi a karbe su.

Punch tace zaman da aka yi a makon jiya shi ne na karshe da za ayi a kan wannan shari’a.

Kara karanta wannan

Baba-Ahmed Ya Gargadi Yan Najeriya Akan Su Guje Wa Yan Takara Masu Nuna Kabilanci da Addini a Zaben 2023

'Yan Boko Haram sun bar kurkuku

Kun ji labari shugaban hafsun tsaro ya yi bayani bayan taron majalisar tsaro a game da mayakan Boko Haram da suka fita daga gidan yarin kirikiri.

Ana zargin ‘yan ta’adda sun samu ‘yanci ne domin ceto fasinjojin jirgin kasan Abuja-Kaduna, Janar Lucky Irabor yace sam ba haka lamarin yake ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng