An yi Garkuwa da Tsohon ‘Dan Majalisar Tarayya da ‘Dan Takaran Sanata Ana Kamfe
- Ana zargin miyagun ‘yan bindiga sun yi garkuwa da Ohaozara Onicha da Linus Abaa Okorie a jihar Ebonyi
- Sai da aka azabtar da Hon. Linus Abaa Okorie, sannan aka yi gaba da shi, yanzu haka yana takaran Sanata a LP
- Shugaban jam’iyyar LP na kasa ya yi kira ga gwamnati da jami’an tsaro suyi kokarin ceto Hon. Linsu Okorie
Ebonyi – Rahotanni sun tabbatar da cewa ‘yan bindiga sun yi awon-gaba da wasu tsofaffin ‘yan majalisar tarayya a garin Ebubeagu da ke jihar Ebonyi.
Vanguard ta kawo rahoto Ohaozara Onicha da Linus Abaa Okorie sun fada hannun ‘yan garkuwa da mutane, wannan lamarin ya auku a karshen makon jiya.
Hon. Ohaozara Onicha da Hon. Linus Abaa Okorie ‘yan siyasa ne da sun taba wakiltar mazabun Ohaozara Onicha da Ivo a majalisar wakilan tarayyan kasar.
Yanzu haka Linus Okorie shi ne mai neman takarar kujerar Sanata a inuwar jam’iyyar Labour Party, LP a mazabar kudancin Ebonyi a zabe mai zuwa.
Rahoton yace ana zargin sai da ‘yan bindigan suka ci zarafin Linsu Okorie, sannan suka tafi da shi zuwa wani wuri da har yanzu ba a sake jin duriyarsa ba.
Dole a fito da Linus Abaa Okorie - LP
Shugaban LP na kasa, Julious Abure ya bukaci a fito da ‘dan siyasar da ya yi shekaru takwas a majalisar tarayyar Najeriya tsakanin 2007 zuwa Mayun 2015.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Kamar yadda wani rahoton ya nuna, Kwamred Abure yace ana neman hana ‘yan takaran jam’iyyarsu ta LP yin kamfe a yankunan Ebonyi da Enugu.
Aikin dakarun Ebubeagu ne
Blueprint tace wani jawabi da ya fito daga David Ogbonna a madadin ‘dan siyasar, ya nuna cewa jami’an tsaron Ebubeagu ake zargin sun dauke ‘dan takarar.
“An yi garkuwa da Hon. Linus Abaa Okorie a safiyar yau (Lahadi) a kan hanyar zuwa gidansa a garin Abakaliki.
Shugaban karamar hukumar Onicha ake zargin ya tura dakarun tsaro na Ebubeagu da suyi wannan danyen aikin.
Bayanan da muka samu sun tabbatar da an galabaitar da shi kamar zai mutu, aka yi masa tsirara, aka dauki hotonsa.
Labarin da ya shigo mana shi ne burinsu su azabtar da shi har ya mutu, sai su jefa gawarsa a cikin rafin Ebonyi.
Ana bibiyar wayoyin Hon. Linus Abaa Okorie
Rahoton ya kara da cewa wayoyin ‘dan takaran suna hannun jagoran ‘yan garkuwa da mutanen da suka dauke shi, kuma ana amfani da su domin gano inda suke.
Da farko an ga alamun cewa wayoyin suna titin Okoja a kusa da hedikwatar ‘yan sanda na jihar, daga baya kuma sai ya nuna yana Ebun-Nwana a garin Edda.
Rikicin APC a Anambra
A makon jiya aka ji labari shugaban Jam’iyyar APC a Anambra, Basil Ejidike ya yi raddi ga Chris Ngige a dalilin kin tallata 'dan takaransu na shugaban kasa.
Ana haka sai Emeka Ibe ya maidawa Basil Ejidike martani, ya wanke tsohon Gwamnan, kuma yace jam’iyyar APC tana hannunsa ne ba su Cif Ejidike ba.
Asali: Legit.ng