Nima Ban Tsira Ba: Wani Gwamnan Najeriya Ya Ce Ambaliyar Ruwa Ta Ci Gidansa

Nima Ban Tsira Ba: Wani Gwamnan Najeriya Ya Ce Ambaliyar Ruwa Ta Ci Gidansa

  • Gwamnan Jihar Bayelsa, Douye Diri na Jihar Bayelsa ya koka kan cewa shima ambaliyar ruwa ta ci gidansa na kansa a garinsu
  • Diri ya bayyana hakan ne a yayin da ya tafi ziyarar gani da ido a wasu garuruwa da ambaliyar ruwa ta shafa a a karamar hukumar Sagbama
  • Diri ya kuma bada tallafin kudi ga mutanen da abin ya shafa ya kuma alkawarin gwamnati za ta turo musu da kayan tallafi

Bayelsa - Gwamna Douye Diri na Jihar Bayelsa ya koka cewa ambaliyar ruwa da ya shafi sassan jihar ya ci gidansa na kansa da ke Sampou a karamar hukumar Kolokuma/Opokuma a jihar.

Diri, wanda ya yi rangadin duba irin barnar da ambaliyar ruwa ta yi a wasu garuruwa ya koka kan wahalhalun da ambaliyar ya jefa mutane ciki, Daily Trust ta rahoto.

Kara karanta wannan

"Najeriya Na Cikin Halin Yaƙi", Sanatan APC Mai Ƙarfin Fada A Ji Ya Yi Magana Mai Ɗaukan Hankali

Flood
Wani Gwamnan Najeriya Ya Ce Shima Ambaliyar Ruwa Ta Ci Gidansa. Hoto: @daily_trust.
Asali: Twitter

Gwamnan ya samu rakiyar kwamishinan muhalli kuma shugaban hukumar kula da ambaliya, Eselema Gbaranbiri, takwaransa na ma'aikatar ayyuka, Moses Teibowei, da Ayibaina Duba da wasu manyan jami'an gwamnati, sun ziyarci garuruwan da ambaliyar ta shafa ciki har da Tungo, Sagabama da Adagbabiri duk a karamar hukumar Sagbama.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Yayin da ya ke yi wa mutane jawabi, gwamnan ya ce yana son ya gani da idonsa abin da mutanen garuruwan ke fuskanta.

Diri ya bada kyautan kudade ga wadanda ambaliya ta shafa

Ya kuma gabatar da kyautan kudi ga garuruwan da abin ya shafa kuma ya yi alkawarin nan take za a turo musu kayan tallafi.

Ya karfafa musu gwiwa duk da cewa ya fahimci suna cikin mawuyacin hali.

Har wa yau, ya yi kira ga yan Bayelsa su rika kula da junansu su taimaka wa wadanda ambaliyar ta shafa.

Kara karanta wannan

Gwamnati ba za ta iya rike jami'o'i ba, ya kamata iyaye su fara kawo tallafi, inji gwamnan APC

Ruwa ba ta tsoron kowa, ni kai na ruwa ya shiga gida na - Diri

Wani sashi na kalamansa:

"Na fito ne domin in gaishe da mutane domin su san cwa gwamnatinsu na tare da su a lokacin da suke fuskantar iftila'i.
"Ruwa ba ya tsoron kowa don ni kai na ruwa ya ci gida na a garin mu. Don haka kowa ya jure ya yi takatsantsan a wannan lokacin musamman mata. Kada yaranku su shiga ruwa. Lokaci ne mai tsauri amma na san Ubangiji zai taimake mu.
"Na bada umurnin a fitar da N450 miliyan don tallafawa mutanen mu, wannan shine mataki na farko. Tunda na ga abin da kai na, za mu kara fitar da wani kudi don mutanen mu su samu abin da za su ci a halin yanzu."

Yadda Wata Baiwan Allah, Ƴayanta 4 Da Ƴar Uwanta Suka Nutse A Gidansu Saboda Ambaliyar Ruwa

A wani rahoton, mutane shida yan gida daya sun nutse bayan ruwa ya mamaye gidansu da karamar hukumar Anambra ta Yamma.

Kara karanta wannan

Buhari Ya Amince a Raba Buhunan Kayan Abinci 240, 000 a Wuraren da Aka Yi Ambaliya

Daily Trust ta tattaro cewa lamarin ya faru ne a garin Nzam da ke karamar hukumar a ranar Talata.

Asali: Legit.ng

Online view pixel