Yadda Wata Baiwan Allah, Ƴayanta 4 Da Ƴar Uwanta Suka Nutse A Gidansu Saboda Ambaliyar Ruwa

Yadda Wata Baiwan Allah, Ƴayanta 4 Da Ƴar Uwanta Suka Nutse A Gidansu Saboda Ambaliyar Ruwa

  • Wata mata da 'ya'yanta hudu da 'yar uwanta sun rasu sakamakon ambaliyar ruwa a karamar hukumar Anambra ta Yamma
  • Wani bidiyo da ya bazu ya nuna wasu matasa a unguwar suna fito da gawarwaki daga gidan da abin ya faru suna kai su tudu
  • A makon da ya gabata ma a kalla mutane guda 81 sun riga mu gidan gaskiya sakamakon hatsarin kwale-kwale a Ogbaru duk a jihar Anambra

Jihar Anambra - Mutane shida yan gida daya sun nutse bayan ruwa ya mamaye gidansu da karamar hukumar Anambra ta Yamma.

Daily Trust ta tattaro cewa lamarin ya faru ne a garin Nzam da ke karamar hukumar a ranar Talata.

Canoe
Yadda Wata Baiwan Allah, Ƴayanta 4 Da Ƴar Uwanta Suka Nutse A Gidansu Saboda Ambaliyar Ruwa. Hoto: @daily_trust.
Asali: Twitter

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Matasa sun ciro gawarwakinsu sun kai su kan tudu

A cewar wani bidiyo da ya bazu, an hangi matasa a garin suna fitowa da gawarwaki daga gidan suna ajiye wa a wani tudu.

A bidiyon, gawarwakin sun hada da na mace daya, yaranta hudu da yar uwanta.

A cewar wanda ke magana a bidiyon, yan gidan suna shirin barin wurin su koma wani wuri ne sai ambaliyar ruwar ya mamaye gidan.

Idan za a iya tunawa a kimanin mutum 81 sun rasa rayyukansu a karamar hukumar Ogbaru ta jihar sakamakon hatsarin jirgin ruwa.

Kuma, wani mutum ya yi nasarar kwashe iyalansa daga ambaliyar ruwan kuma ya koma ya kula da wurin amma ya nutse a Ogbaru yayin da ya ke barci.

Anambra: NEMA ta fara aikin ceto rayyuka a yankunan da ambaliyar ruwa ya sha

Hukumar bada agajin gaggawa ta kasa, NEMA, a yayin taron manema labarai ta ce ta fara zagayen sa ido a jirgi mai saukan ungulu don ceto mutanen da suka makalle a gidajensu sakamakon ambaliyar ruwan.

Hankula Sun Tashi Yayin Da Aka Nemi Mutum 30 Aka Rasa Sakamakon Kifewar Kwale-Kwale A Wata Jihar Najeriya

A wani rahoton, a kalla mutane 30 ne aka ce sun ɓace a yayin da kwale-kwale da ke dauke da mutane 50 ya kife a garin Umunnankwo da ke karamar hukumar Ogbaru na jihar Anambra.

Abin bakin cikin ya faru ne a ranar Juma'a 7 ga watan Oktoba, Daily Trust ta rahoto.

Asali: Legit.ng

Online view pixel