Buhari Ya Amince a Raba Buhunan Kayan Abinci 240, 000 a Wuraren da Aka Yi Ambaliya

Buhari Ya Amince a Raba Buhunan Kayan Abinci 240, 000 a Wuraren da Aka Yi Ambaliya

  • Gwamnatin Muhammadu Buhari ta yarda a raba kayan abinci a wuraren da ake fama da ambaliyan ruwa
  • Ambaliyan da aka yi a bana ya shafi jihohi 27, don haka gwamnatin tarayya take bada agajin gaggawa
  • Zuwa yanzu sama da mutum 500 sun mutu, baya ga gidaje da-dama da gonaki da aka yi asara a Najeriya

Abuja - Shugaba Muhammadu Buhari ya amince a raba metric ton 12, 000 na hatsi ga mutanen da ambaliyar ruwa ta rutsa da su a jihohin kasar nan.

Daily Trust tace Darekta Janar na hukumar NEMA mai bada agajin gaggawa, Mustapha Habib Ahmed ya bada wannan sanarwa a ranar Alhamis.

Sanarwar ta fito ne wajen bikin tunawa da ranar rage masifa na Duniya wanda aka yi a garin Abuja.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Gwamnan PDP Ya Nada Sabbin Hadimai 28,000, Ya Ware Makudan Kudin Tallafawa Mutane

Mustapha Habib Ahmed ya bayyana cewa hukumar NEMA sun fara aikawa da kayan bada tallafi zuwa wuraren da ambaliya tayi barna kwanan nan.

Duk da ana samun matsala wajen bin hanyar Lokoja, shugaban NEMA yace sun hada-kai da jami’an tsaro domin a iya aika kaya zuwa jihar Kogi.

Abin da ya jawo ruwa ya yi gyara

A cewar Mustapha Habib Ahmed, ruwa ya yi barna sosai a shekarar nan ne saboda mutane sun yi watsi da gargadin da aka yi masu tun a farkon damina.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ambaliya
Ambaliyar ruwa a Najeriya Hoto: www.pulse.ng
Asali: UGC

An rahoto Ahmed yana cewa gwamnatin tarayya ta ankarar da Jihohi da kananan hukumomi game da hadarin zabe a wuraren da ruwa zai iya barkowa.

Minista ta bayyana halin da ake ciki

Leadership tace Mista Ali Grema ya samu wakiltar Ministar bada tallafi, agajin gaggawa da jin-kai, Sadiya Umar-Farouk wajen taron da aka yi a Abuja.

Kara karanta wannan

Zan Tabbatarwa 'Yan Najeriya Tsaro Kafin Na Mika Mulki, Buhari Ya jaddada

Ministar tace an rasa rayuwa fiye da 500, kuma ambaliyar shekarar nan ta shafi mutum sama da miliyan 1.4, bayan gidaje 90, 000 da suka rushe ko lalace.

Har ila yau, Mai girma Ministar tace gonakin mutane sun lalace a dalilin ambaliyar. Tasirin hakan zai iya zama an samu karancin abinci a Najeriya da Afrika.

Ambaliyar ruwan da aka yi wannan shekaran ya shafi jihohi 27 da birnin tarayya Abuja

Za a raba metric ton 12, 000 na buhunan abinci a jihohin, kimanin buhuna 240, 000 kenan. Leadership tace tireloli 400 za a bada da nufin a rage radadin jama'a.

Daliban Yauri suna tsare har yau

Yadda aka ceto ragowar fasinjojin jirgin kasan Kaduna-Abuja, kun ji labari kungiyar PTAN tana so a kubutar da ‘yan makarantar Yauri da aka dauke tun a 2021.

Shugaban PTAN na kasa, ya yi kira ga gwamnati tayi amfani da hikima da dabara da salon da tayi amfani da su wajen ceto fasinjoji, domin kubutar da ‘daliban.

Kara karanta wannan

Tsohon Gwamnan Arewa Da Buhari Ya Yi Wa Afuwa Ya Fadi Yadda Za'a Kawo Karshen Cin Hanci da Rashawa a Najeriya

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng