Da Dumi-Dumi: Gwamnan PDP Ya Nada Sabbin Hadimai 28,000, Ya Ware Makudan Kudin Tallafawa Mutane

Da Dumi-Dumi: Gwamnan PDP Ya Nada Sabbin Hadimai 28,000, Ya Ware Makudan Kudin Tallafawa Mutane

  • Gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas ya sake nada sabbin hadimai 28,000 tare da ware makudan kudade ga wadanda ambaliyar ruwa ya ritsa da su
  • Hakan na zuwa ne kwana daya bayan gwamnan ya nada hadimai 14,000 wanda ya haddasa cece-kuce
  • Mai magana da yawun gwamnan, Kelvin Ebiri, ne ya sanar da hakan a cikin wani jawabi da ya saki a ranar Laraba, 12 ga watan Oktoba

Rivers - Gabannin babban zaben 2023, gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike ya sake nada wasu sabbin mukaman siyasa 28,000.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da kakakin gwamnan, Kelvin Ebiri, ya saki a ranar Laraba, 12 ga watan Oktoba, Channels tv ta rahoto.

Nyesom Wike
Da Dumi-Dumi: Gwamnan PDP Ya Nada Sabbin Hadimai 28,000, Ya Ware Makudan Kudin Tallafawa Mutane Hoto: Thisday
Asali: UGC

Nadin wanda ya fara aiki nan take na zuwa ne kwana daya bayan Wike ya nada hadimai 14,000, da jami'an hadin gwiwa na gudunma 319 da wasu 40 na karamar hukuma.

Kara karanta wannan

Tsohon Gwamnan Arewa Da Buhari Ya Yi Wa Afuwa Ya Fadi Yadda Za'a Kawo Karshen Cin Hanci da Rashawa a Najeriya

A cewar sanarwar, gwamnan ya kuma ware zunzurutun kudi naira biliyan daya don tallafawa wadanda ambaliyar ruwa ya cika da su a jihar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ebiri ya bayyana cewa kudaden an ware su ne don tallafawa mutanen da ambaliyar ruwa ya ritsa da su a yankunan Ahoada ta yamma da Ogba/Egbema/Ndoni da ke jihar.

Ya ce an shirya hakan ne "domin ba iyalai marasa galihu musamman a Ahoada ta yamma da Ogba/Egbema/Ndoni wadanda sune abun yafi shafa damar ci gaba da rayuwa duk da ambaliyar ruwa wanda ya shafe gidaje gonaki da tursasawa mazauna yankunan sauya muhalli zuwa tudun na tsira."

Musamman Wike ya ce sakataren din-din-din na ayyuka na musamman a ofishin sakataren gwamnatin jihar Ribas, Dr. George Nwaeke, shine zai jagoranci kwamitin, yayin da Misis Inime I. Aguma, ita ce sakatariya.

Sauran mambobin kwamitin sune shugaban karamar hukumar Ahoada ta yamma, Hon. Hope Ikiriko, shugaban karamar hukumar Ogba/Egbema/Ndoni, Hon. Vincent Job, Hon. Chukwuemeka Onowo da daraktan gudanarwa na ma'aikatar ayyuka na musamman.

Kara karanta wannan

Kano: Gini Mai Hawa Ɗaya Ya Rufta Wa Yara 3 Yan Gida Daya, Biyu Cikinsu Sun Mutu

Ana sanya ran dukka mambobin kwamitin zasu gana da Wike a ranar Alhamis a gidan gwamnatin jihar Ribas da ke Port Harcourt, rahoton PM News.

Tsohon Gwamnan Da Buhari Ya Yi Wa Afuwa Ya Fadi Yadda Za'a Kawo Karshen Cin Hanci da Rashawa a Najeriya

A wani labarin, tsohon gwaman jihar Plateau, Joshua Dariye, ya bayyana cewa za a iya kawo karshen cin hanci da rashawa a kasar nan idan har kowani dan Najeriya zai bayar da hadin kai.

Sanatan ya bayyana hakan ne a a ranar Litinin, yayin wata hira da gidan talbijin din Channels a shirin NewsNight.

Dariye ya kuma bayyana cewa hukunta shi da aka yi tare da tsohon gwamnan jihar Taraba, Jolly Nyame, kan aikata rashawa bai kawo karshen sama da fadi da ake yi kan dukiyar kasar ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel