Fasinjoji 13 Sun Kone Kurmus a Wani Hadarin Mota da Ya Rutsa da Su a Enugu

Fasinjoji 13 Sun Kone Kurmus a Wani Hadarin Mota da Ya Rutsa da Su a Enugu

  • Rahoton da muke samu daga jihar Enugu ya bayyana cewa, wasu Hausawa sun yi hadari sun kone kurmus
  • Akalla mutane 13 ne suka mutu a hadarin da ya faru a jiya Lahadi 30 ga watan Oktoba, inji majiyoyi
  • Ana yawan samun hadurra a kan titunan Najeriya, musamman yayin tafiya a motocin kasuwanci

Jihar Enugu - Akalla fasinjoji 13 ne suka kone kurmus a wani hadarin motan da ya faru a kusa da Four-Corners Enugu da misalin karfe 9 na daren jiya Lahadi, inji rahoton Vanguard.

An ruwaito cewa, motar mai daukar mutane 14 ta taso ne daga jihar Imo a Kudanci inda ta nufi jihar Adamawa a Arewacin Najeriya.

Rahotanni sun bayyana cewa, motar ta shigewa wata babban tirela ne kafin daga bisani ta kama da wuta.

Mota ta kone da Hausawa a jihar Enugu
Fasinjoji 13 sun kone kurmus a wani hadarin mota da ya rutsa da su a Enugu | Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

Dukkan fasinjojin dake ciki sun kone kurmus kuma sun mutu face mutum daya da ya kone, shima ba a iya gane shi.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Yadda ya tsira daga hadarin

Wasu majiyoyi sun bayyana cewa, ya yi tsalle ne ya fice daga motar yayin da ta fadi, wasu kuwa suka ce mutanen dake gefe ne suka ciro shi daga cikin motar.

Channels Tv ta tattarp cewa, mutumin da ya tsiran yanzu haka yana can kwance a asibitin koyarwa na jami'ar Najeriya ta Nsukka dake Ituku-Ozalla a jihar.

Da yake tabbatar da faruwar lamarin, kwamandan yanki na hukumar kula da haddura ta kasa a Enugu, Joseph Toby ya ce hukumar ta kan gargadi direbobi game da tafiye-tafiye cikin dare.

Toby ya kuma bayyana cewa, mutumin da ya tsira a yanzu haka yana asibiti yana karbar kulawar likita.

Ya kuma bayyana cewa, mutanen da hadarin ya rutsa dasu Hausawa ne, domin wasu Hausawa sun nemi a basu damar yi musu jana'iza.

Sojoji Sun Kashe `Yan Boko Haram 8 a Neja Bayan Wani Hari da Suka Kai a Barikin Soja

A wani labarin, akalla 'yan ta'adda takwas aka hallaka da ake zargin 'yan Boko Haram ne a yankin New Bussa a karamar hukumar Borgu ta jihar Neja, inji rahoton Tribune Online.

Rahoton da muka samo ya bayyana cewa, wannan lamari ya faru ne a karshen mako bayan da 'yan ta'addan suka kai farmaki barikin soja a yankin don kubutar da 'yan uwansu dake tsare.

A cewar wasu rahotanni, an kuma kama wasu tsageru uku daga cikinsu, sai dai an ruwaito cewa, wasu daga jami'an sojojin sun samu raunuka a rikicinsu da 'yan ta'addan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel