Budurwa Ta Kai Kaninta Jami'a Cotonou, Ta Yi Masa Rijistar N210k

Budurwa Ta Kai Kaninta Jami'a Cotonou, Ta Yi Masa Rijistar N210k

  • Wata budurwa 'yar Najeriya ta yada bidiyon yadda ta tattara kaninta ta kai shi Cotonou, jamhuriyar Benin domin ci gaba da karatunsa
  • Ta ce ta yi masa rajista a wata jami'a a can, ta kuma bayyana cewa, jamhuriyar Benin kasa ce mai kyau
  • Bayan yaa bidiyon, mutane da dama a kafar sada zumunta sun fara tambayarta kan bayanai game da makarantar da kuma nawa ake biya

Bidiyon wata budurwa 'yar Najeriya da ta yiwa kaninta rajistar makaranta a jami'ar Cotonou ya yadu a intanet, jama'a da dama sun tofa albarkacin bakinsu.

A cewar budurwar, kungiyar malaman jami'o'i ta ASUU ba za ta hana kaninta kammala karatu ba duk da cewa ba za su janye yajin aiki ba.

Budurwa ta kai kaninta karatu Cotonou, ta ba da labari
Budurwa Ta Kai Kaninta Jami'a Cotonou, Ta Yi Masa Rijistar N210k | Hoto: TIkTok/@abeehorlahmorwhom
Asali: UGC

Ta ce ita da kaninta nata sun hau babur ne daga Legas ta hanyar Idi-Iroko, suka hau mota har dai suka shiga kasar ta Benin.

Kara karanta wannan

Mawakiyar Najeriya Ta Ki Shan Hannu Da Buhari Yayin Gabatar Mata Da Lambar Yabo, Jama’a Sun Yi Cece-Kuce

Bayan da ta yada bidiyon, jama'a da dama sun tambaye ta karin bayani game da kudin jami'ar, sannan ta fara basu bayanin ta kashe N210k a rajista kawai.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A cewarta:

"Ga wadanda ke tambayar kudin makaranta: Kudin fom N10k. Rajista da karbar takardar amincewa N51k. Kudin makaranta N150k. Wannan ne jumillar abin da muka kashe.

Kalli bidiyon:

Martanin 'yan soshiyal midiya

@Claris cray tace:

"Kudin ne ni ya dame ni. Najeriya kasa ta. Na yi kewar Benin.

@user606309 yace:

"Tabbas haka ne abin da ya faru dani lokacin da nake dawowa gida daga Ghana na tsorata yayin wuce wasu kananan kauyuka.

@Blue yace:

"Zan so sanin karin bayani game da makarantar da kuma tsarinta da abin da ake bukata."

@Aye Dido Lee yace:

"Woow...Kenan akwai wata hanyar zuwa Benin ba ta Badagry ba?"

Kara karanta wannan

Bidiyo: 'Yar Najeriya ta mutu yayin da ake mata tiyatar cikon mazaunai a India

@irabor amiohu yace:

"Irin wannan lamari ya bani annashuwa nima."

@Belladonna tace:

"Barka da zuwa Cotonot, kasarmu kyakkyawa."

Bidiyon Malamin Makarantan da Yaje Banki da 'Ghana-Must-Go' don Karbar Albashinsa na Wata 8 Ya Ba Da Mamaki

A wani labarin, 'yan soshiyal midiya sun yi martani ga bidiyon wani mutumin da aka gani a banki dauke da jakar 'Ghana Must Go' rataye a kafadarsa.

A cewar @nanahook00, wacce ta yada bidiyon a TikTok, mutumin malamin makaranta ne, kuma ya zo da jakar ne domin karbar albashinsa na wata takwas da yake bin gwamnati.

A cikin bidiyon mai tsawon dakiku 10, an ga lokacin da malamin ke muzurai a cikin bankin, ya kuma nuna kamar ba komai yayin da yake harkar dake gabansa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.