Bidiyon Wata ‘Yar Najeriya Ta Mutu Yayin da Ake Yi Mata Cikon Mazaunan Roba a India

Bidiyon Wata ‘Yar Najeriya Ta Mutu Yayin da Ake Yi Mata Cikon Mazaunan Roba a India

  • A garin neman gira wata 'yar Najeriya ta rasa ido, Allah ya dauki ranta ana tsaka da yi mata tiyatar cikon mazaunai
  • Wata majiya da ta tabbatar da faruwar lamarin ya yada hotunan budurwar, wacce aka ce 'yar kasuwa ce
  • 'Yan mata da samari na yawan zuwa asibiti don neman gyarawa ko tada komada a jikinsu, lamarin da ka iya zuwa tsaiko wasu lokutan

India - Wata tsaleliyar budurwa 'yar Najeriya mai shekaru 28, Amelia Pounds ta riga mu gidan gaskiya yayin da yi mata aikin gyaran jiki a kasar India

An ruwaito cewa, budurwar 'yar kasuwa ta sheka ne yayin da ake kan yi mata tiyatar cikon mazaunai a wani asibitin da a bayyana sunansa ba a birnin New Delhi a ranar Juma'a 7 ga watan Oktoba da safe.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Watanni Kafin Ya Sauka a 2023, Wami Gwamnan PDP Ya Naɗa Sabbin Hadimai 14,000

Yada 'yar Najeriya ta sheka garin tiyatar cikon mazauni
Bidiyon Wata ‘Yar Najeriya Ta Mutu Yayin da Ake Yi Mata Cikon Mazaunan Roba a India | Hoto: lindaikejisblog.com
Asali: UGC

Wani mai amfani da shafin Twitter ya tabbatarwa wata ma'abociya kafafen sada zumunta, Vera Sidika labarin, inji kafar labarai ta Linda Ikeji.

Ba sabon abu bane a duniya a samu mata da maza dake zuwa asibiti domin sauyawa ko gyara wani sashen jikinsu da suke ganin bai musu ba.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ga dai bdiyon budurwar da ta gangara kiyama a garin neman kiba:

Martanin jama'a

Yayin da AnyiWise Tv ya yada bidiyon budurwar a Facebook, jama'a da dama sun bayyana martaninsu ga wannan bidiyo mai cike da ban mamaki.

Sonia Alfred tace:

"Haka suke samun kudi kamar wannan sai su rasa me za su yi dashi.. a madadin taimakawa mabukata za su yi amfani dasu wajen shirme duk da sunan kwalliya..."

Austin Nelson yace:

"Ta samu kudi sai ta tafi India cikon mazaunai, abin tausayi, Maimakon ta yi amfani da mai kadai."

Kara karanta wannan

Da Sauran Aiki: Sanatar PDP Ta Gano Katuwar Matsala a Cikin Kasafin Kudin 2023

Recheal Nkwor tace:

"Me zaki cewa ubangiji yanzu. Allah ya jikanki, wasu sa shiga taitayinsu."

Jane Micheal Blessed tace:

"Kalli birkitaccen asibitin ma tukuna."

Shirin BBNaija Wakili Ne Na Shaidan a Doron Kasa, Inji Kungiyar MURIC

A wani labarin, kungiyar kare hakkin musulmai ta MURIC ta goyi bayan batun Segun Runsewe na cewa majalisar dokokin kasa ta ba hukumar al'adu ta kasa (NCAC) ikon ji da lamarin BBNaija domin dakile yaduwar tsiraici.

Wannan batu na goyon baya na kunshe ne a cikin wata sanarwa da daraktan MURIC, Farfesa Ishaq Akintola ya fitar a yau Lahadi 9 ga watan Oktoba.

Darakta janar na NCAC ya bukaci majalisar dokokin kasar nan da ta ba hukumarsa damar tunkarar shirin BBNaija don dakile yaduwar tsiraici a kasar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel