Kudin da Aka Kashewa Wajen Kula da Jirage 10 a Fadar Shugaban Kasa Ya Haura N80bn

Kudin da Aka Kashewa Wajen Kula da Jirage 10 a Fadar Shugaban Kasa Ya Haura N80bn

  • Makudan kudin da gwamnatin tarayya take kashewa kan jiragen fadar shugaban kasa ya karu sosai
  • Daga shekarar 2016 zuwa yau, jirage 10 da ke fadar shugaban Najeriya sun lakume Naira biliyan 81.8
  • Muhammadu Buhari ya yi alkawarin zai rabu da wasu jiragen, amma har yanzu ba ayi hakan ba

Abuja - Kasafin da ake yi wa jiragen fadar shugaban Najeriya ya karu da 121% a shekaru takwas. Wani rahoto da Punch ta fitar yau ya tabbata da haka.

Daga shekarar 2016 zuwa yanzu, gwamnatin tarayya ta ware Naira Biliyan 81.80 ga jiragen fadar shugaban kasa domin dawainiya da kuma kula da su.

Da wadannan jiragen ne Mai girma shugaba Muhammadu Buhari da ‘yan tawagarsa suke amfani a duk lokacin da za suyi tafiya a gida da kasashen waje.

Binciken ya nuna daga cikin wannan kudi aka ware Naira biliyan 62.47 domin kula da aikin jiragen. A duk shekara abin da ake kashewa yana kara tashi.

Kara karanta wannan

Kasafin Kuɗi 2023: Kudi N22.44Bn gwamnatin tarayya ke shirin kashewa yan gidajen yari

Sannan an kashe kimanin Naira biliyan 17 wajen tafiye-tafiye da ake yi a cikin gida da kuma wajen Najeriya. An kashe Naira biliyan 2.04 a wasu abubuwan.

Tun da Muhammadu Buhari ya zama shugaban kasa a Mayun 2015, gwamnatin Najeriya take dawainiya da jiragen sama 10 da ke fadar shugaban kasa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Fadar Shugaban Kasa
Buhari da iyalinsa a jirgin sama Hoto: www.36ng.ng
Asali: UGC

Jiragen da Najeriya take da su

Jiragen nan sun hada da Boeing Business Jet (Boeing 737-800 da NAF 001), Gulfstream 550, Gulfstream V (Gulfstream 500), sai Falcons 7X biyu.

Akwai jirgin Hawker Sidley 4000, jiragen AgustaWestland AW 139 masu saukar ungulu biyu, da wasu jiragen biyu kirar AgustaWestland AW 101.

Alkawarin da Buhari ya yi

Kafin ya hau mulki, Buhari ya yi alkawari Gwamnatinsa za ta rage adadin jiragen fadar shugaban kasa domin a rage facakar kudin da Najeriya ke yi.

Kara karanta wannan

Taliyar karshe: An gano biliyoyin da Buhari da Osinbajo za su ci da sunan kudin abinci da hawa jirgi

Shekaru bakwai da rabi kenan har yau ba a cika wannan alkawari ba. An nemi a saida jiragen Falcon 7x da Hawker 4000 a 2016, sai aka yi tayin banza.

A Satumban 2020, gwamnatin tarayya ta sa jirgin Hawker 4000 mai lamba 5N-FGX/: RC 066 a kasuwa, zuwa yanzu ba a san ya ake kare da maganar ba.

PDP ta fara kamfe a Akwa Ibom

Kuna da labari jiragen sama akalla 15 sun sauka a babban filin jirgin saman Victor Attah da ke garin Uyo a farkon makon nan yayin da PDP ta fara kamfe.

Gwamnoni da sauran manyan jam’iyyar PDP sun je Akwa Ibom domin kaddamar da yakin neman zaben Atiku Abubakar da Ifeanyi Okowa a zaben 2023.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng