Fadar Shugaba Buhari Za Ta Kashe N14bn a Matsayin Kudin 'Data' da Katin Waya

Fadar Shugaba Buhari Za Ta Kashe N14bn a Matsayin Kudin 'Data' da Katin Waya

  • Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gabatar da kasafin kudin 2023, an bayyana inda za a kashe kudade
  • Gwamnatin Najeriya ta ware biliyoyi domin sayen data, katin waya da ruwa a fadar shugaban kasa ta Aso Rock Villa
  • 'Yan Najeriya na ci gaba da tura baki tun bayan gabatar da kasafin kudin 2023 da zai ci Naira tirilliyan 20.51

FCT, Abuja - Fadar shugaban kasa ta shirya kashe N14.8bn domin sayen datan hawa shafukan yanar gizo, takardu da sauran kudaden da suka shafi katin waya da na'ura mai kwakwalwa a kasafin kudin 2023 da Buhari ya gabatar.

A cikin kasafin kudin, an ce 'data' kadai za a ci na N67.1m a Villa, yayin da takardu da sauran abubuwan da na'ura mai kwakwalwa za ta ci zai kai N79m.

Kara karanta wannan

Kasafin Kuɗin 2023: An Ware N1.6bn Don Ciyar da Daliban Firamare Da TraderMoni

Gwamnati ta bayyana kudin data da za a ci a fadar Buhari
Fadar Shugaba Buhari Za Ta Kashe N14bn a Matsayin Kudin Data da Katin Waya | Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Fashin bakin kasafin kudin ya kuma nuna cewa, za a kashe N35.9m don biyan kudin wutar lantarki yayin da cajin katin tangaraho da ruwan famfo zai ci N306.2m, N6m da N40.6m bi da bi.

Daga jumillar kasafin kudin, za a kashe N1.6bn kan ma'aikata, inji rahoton Punch.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Hakazalika, an ware N35m domin kashe su a sayen littatafai da jaridu, inda jaridu za su ci N26.m littatafai kuma za su lashe N8.6m.

Buhari ya gabatar da kasafin kudin 2023

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gabatar da kasafin kudin 2023 a gaban gamayyar majalisar dattawa da ta wakilai a makon jiya.

Kasafin kudin ya nuna cewa, ana bukatar kashe Naira tiriliyan 20.51 a shekara mai zuwa, wacce Buhari zai sauka.

Legit.ng Hausa ta tattaro cewa, kasafin kudin 2023 ya dara na 2022 da zunzurutun kudi N750bn, inda a 2022 aka nufi kashe N19.76tr.

Kara karanta wannan

Kasafin Kuɗi 2023: Kudi N22.44Bn gwamnatin tarayya ke shirin kashewa yan gidajen yari

'Yan Najeriya na ci gaba da nuna damuwa game da kasafin kudin kasar, inda suke tsokaci da yawan kudin da ake son kashewa ga kuma tarin bashi da ake bin kasar.

Buhari Da Osinbajo Za Su Kashe N11.92bn Wajen Cin Abinci Da Zirga-Zirga

A wani labarin, bincike ya nuna cewa, kasafin kudin 2023 da shugaban kasan Najeriya Muhammadu Buhari ya gabatar a makon jiya ya bayyana adadin kudaden da ofishinsa da na mataimakinsa za su ci a fannin tafiya da abinci kadai ya zarce N11.92bn a shekarar.

Tafiye-tafiyen da ake nufi anan na cikin gida ne da wajen kasa, kamar yadda rahotanni suka bayyana.

Jaridar Punch a yau Lahadi 9 ga watan Oktoba ta bayyana cewa, an ware N1.58bn domin kula da lafiyar jiragen sama, yayin da aka ware N1.60bn domin gyara injunan jiragen Gulfstream GV da CL605.

Asali: Legit.ng

Online view pixel