Manoma Sun Roki Gwamnatin Buhari Ta Sanya Dokar Hana Shigo da Alkama

Manoma Sun Roki Gwamnatin Buhari Ta Sanya Dokar Hana Shigo da Alkama

  • Kungiyar manoma, masu sarrafawa da dillalan alkama a Najeriya sun roki a sanya dokar hana shigo da alkama kasar
  • Kungiyar ta ce akwai bukatar a wadatar 'yan Najeriya a harkar samar da alkama amma daga noman cikin gida
  • Shugaban kungiyar na kasa, Alhaji Adamu Ardo ya kuma bukaci gwamnati ta kawo hanyoyin habaka noman alkama a kasar

Kungiyar manoma, masu sarrafawa da dillalan alkama a Najeriya (NAWFPMAN) ta tabbarwa 'yan Najeriya iya samar da hekta 200,000 na alkama ta hanyar tallafin babban bankin Najeriya (CBN).

Kungiyar wacce ke kira ga sanya dokar hana shigo da alkama ta bayyana hakan ne a Abuja a ranar Asabar 8 ga watan Oktoba.

Manoma na neman a hana shigo da alkama Najeriya
Manoma Sun Roki Gwamnatin Buhari Ta Sanya Dokar Hana Shigo da Alkama | Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

Wakilin Legit.ng da ya halarci taron da kungiyar ke wannan batu ya ji tana cewa, akwai bukatar cike bukatun 'yan Najeriya na alkama ta hanyar noma a cikin gida ba tare da an shigo da kaya ba.

Kara karanta wannan

Shirin shaidanu ne: MURIC ta goyi bayan a kawo karshen 'shirin tsiraici na BBNaija'

Mambobin kungiyar a baya sun ci gajiyar shirin rancen gwamnatin tarayya na Anchor Borrowers (ABP) da babban bankin Najeriya (CBN) ya samar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A habaka noman alkama

Shugaban kungiyar na kasa, Alhaji Adamu Ardo ya kuma bukaci gwamnatin Buhari da ta kawo hanyar habaka noman alkama a kasar.

Ya ce hakan zai taimaka wajen warware matsalolin shigo da alkama kasar tare da rage farashin alkamar da abincin da ake samarwa daga ita a Najeriya.

Da yake karin haske, ya kuma bayyana cewa, kungiyar da mambobinta sun samar da hekta sama da 15,000 na alkama a noman ranin bara.

Ya kuma bayyana cewa, gudunmawar da kungiyar da mambobinta suka bayar na samar da alkama ya rage yawaitar shigo da alkama Naejeriya.

A cewarsa, ya kamata gwamnati ta karfafa gwiwar mambobin kungiyar ta hanyar sanya dokar hana shigo da alkama kamar yadda ta yi kan shigo da shinkafa.

Kara karanta wannan

Mun Kashe Dala Miliyan 10 Don Ciyar Da Ɗalibai Miliyan 10, In Ji Gwamnatin Tarayyar Najeriya

Najeriya Ba Za Ta Tsira Ba Idan Aka Zabi Shugaba Kamar Buhari a 2023, Inji Dattijon Arewa

A wani labarin, mai magana da yawun majalisar dattawan Arewa, Dakta Hakeem Baba-Ahmad ya bayyana cewa, bai dace Najeriya ta samu shugaba mai irin halayen Buhari ba, kuma dole shugaban Najeriya na gaba ya sha bamban da akidun Buhari.

Baba-Ahmad ya yi wannan tsokaci ne a wata tattaunawa da jaridar Punch da aka buga a ranar Lahadi 9 ga watan Oktoba.

Da yake koka yadda mulkin Buhari ya kasance, Baba-Ahmad ya ce:

“Bana tunanin za mu tsira na tsawon shekaru goma tare idan muka ci gaba da tafiya yadda muke a karkashin Buhari."

Asali: Legit.ng

Online view pixel