NDIC Na Son Ƴan Najeriya Da Ke Da Kuɗi A Wasu Bankunan Kasuwanci 20 Da Suka Durƙushe Su Taho Su Karɓi Kuɗinsu

NDIC Na Son Ƴan Najeriya Da Ke Da Kuɗi A Wasu Bankunan Kasuwanci 20 Da Suka Durƙushe Su Taho Su Karɓi Kuɗinsu

  • Yan Najeriya da ke ajiyar kuɗaɗen su a wasu bankunan kasuwanci guda 20 da suka durƙushe suna da daman zuwa su karbi Kuɗinsu
  • Hukumar da NDIC ta bada tabbacin cewa babu wanda kudinsa zai yi ciwon kai kuma duk mai zuwa karban Kudi ya gabatar da ingantaccen shaida
  • Ɗaya daga cikin abubuwan da ke damun yan Najeriya masu ajiyar kuɗi a banki shine tabbatar da tsaron kudinsu

Abuja - Hukumar kula da hakkokin masu ajiya a bankunan kasar nan (NDIC), da ke karkashin Ma'aikatar Kudi, ta kwato kudaden kwastomomi da ke ajiya a wasu bankuna 20 da suka durƙushe.

Bello Hassan, shugaban kuma babban direktan hukumar ne ya bayyana hakan yayin da ke jawabi a Abuja wurin taron bajekolin kasa da kasa.

Banki
NDIC Na Son Ƴan Najeriya Da Ke Da Kuɗi A Wasu Bankunan Kasuwanci 20 Da Suka Durƙushe Su Taho Su Karɓi Kuɗinsu. Hoto: Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kara karanta wannan

Rikicin PDP: "Ni Ba Waliyyi Bane, Ina Da Nakasu Da Dama", Ayu Ya Yi Martani Kan Zargin Rashawa Da Wike Ya Masa

Leadership ta rahoto cewa Hassan ya bayyana kwato kudaden da NDIC ta yi a matsayin cika alkawari da hukumar ta yi na cewa za ta kare kwastomomi idan banki ya durƙushe.

Shugaban na NDIC, wanda ya samu wakilcin direktan ayyuka a hukumar, Nuhu Bashi, ya yi alkawarin biyan kudaden baki daya ga duk wani kwastoma da ya taho don karban kudinsa.

Kalamansa:

"Abin da wannan ke nufi shine, domin jajircewar mu wurin sauya kadarori zuwa kudi, hukumar ta samu isasun kudi da za ta biya dukkan kwastomomi da kudinsu suka maƙalle a bankunan da suka durƙushe."

Jerin bankunan da suke durƙushe a Najeriya

Bankunan da abin ya shafa sune ABC Merchant Bank Limited; Allied Bank of Nigeria; Alpha Merchant Bank Pic.; Amicable Bank of Nig. Limited; Commerce Bank; Commercial Trust Bank Limited; Continental Merchant Bank Pic.: Cooperative & Commerce Bank Plc da Eagle Bank; Financial Merchant Bank Limited.

Kara karanta wannan

Yadda Hadimin Gumi ya Dinga Tarwatsa Kokarin FG na Ceto Fasinjojin Jirgin Kasa, Jami’i

Saura sune Icon Limited (Merchant Bank); Ivory Merchant Bank; Kapital Merchant Bank Limited; Mercantile Bank of Nig. Plc.; Merchant Bank of Africa Limited; Nigeria Merchant Bank Plic.; Pan African Bank Limited; Premier Commercial Bank Limited; Progress Bank of Nigeria; da Rims Merchant Bank Limited.

Abin da kwastomomin bankunan da suka durƙushe za su yi?

NDIC ta yi kira ga masu ajiyar kuɗi, masu bada bashi, da masu hannun jari a bankunan da aka lissafa wadanda suka durƙushe su tafi kafafen da hukumar ta umurta su nuna shaida don karban kudinsu, The Guardian ta rahoto.

Hassan ya ce:

"An tura sakonni ga masu bada bashi na bankuna bakwai na ajiyar kuɗi (DMBs) da aka sayar da kadarorinsu da masu ajiyar kuɗi da tsaffin ma'aikatan ƙananan bankuna (MFBs) da bankunan samar da gidaje (PMB) su taho don karbar kuɗinsu da suka maƙalle a bankunan da suka durƙushe.
"Wanda abin ya shafa suna iya ziyartar ofishin hukumar mafi kusa da su ko su yi amfani da manhajar NDIC ta yanar gizo ko su ziyarci shafinmu na intanet: www.ndic.gov.ng, don bin hanyoyin yadda za su karbi kudinsu."

Kara karanta wannan

Bakano ya girgiza intanet, ya kera keke napep din da ta ba 'yan Najeriya mamaki

Mun Kashe Dala Miliyan 10 Don Ciyar Da Ɗalibai Miliyan 10, In Ji Gwamnatin Tarayyar Najeriya

A wani rahoto, Gwamnatin tarayyar Najeriya ta ce ta kashe kimanin Dalar Amurka Miliyan 10 don ciyar da yaran Najeriya karkashin shirin National School Feeding Programme.

Wannan na cikin wani yunkuri ne na kawar da bautar da kananan yara a kasar, Premium Times ta rahoto.

Chris Ngige, ministan Kwadago da samar da ayyuka ne ya bayyana hakan yayin da ya karbi bakuncin jakadar Amurka a Najeriya, Mary Leonard, da wasu jami'an gwamnatin Amurka da suka kai masa ziyarar ban girma a ranar Juma'a.

Asali: Legit.ng

Online view pixel