'Na Kasa Samun Natsuwa': Dan Shekara 18 Da Ya Kashe Mahaifiyarsa Don Ta Kira Shi Shege Ya Fallasa Kansa

'Na Kasa Samun Natsuwa': Dan Shekara 18 Da Ya Kashe Mahaifiyarsa Don Ta Kira Shi Shege Ya Fallasa Kansa

  • Wani matashi dan shekara 18, Tope Momoh, ya tona kansa cewa shi ya halaka mahaifiyarsa cikin dare saboda ta kira shi 'shege'.
  • Tope, ya fada wa kotu cewa ya kasa samun natsuwa ne a rayuwa tun bayan da aka birne mahaifiyarsa dole ta sa ya fallasa kansa
  • Matashin ya kuma rokon kotun ta yi masa sassauci si dai alkali bai amsa rokon ba, ya umurci a bashi masauki a gidan gyaran hali

Jihar Ondo - Wani matashi dan shekara 18 mai suna Tope Momoh ya shake mahaifiyarsa har sai da ta ce ga garinku saboda ta kira shi shege.

Tope ya amsa cewa ya halaka mahaifiyarsa mai suna Stella, makonni biyu bayan an birne ta, The Nation ta rahoto.

Kara karanta wannan

Mummunan Hatsarin Mota Ya Faru A Jigawa, An Rasa Rayyuka

Kotun
'Na Kasa Samun Natsuwa': Dan Shekara 18 Da Ya Kashe Mahaifiyarsa Don Ta Kira Shi Shege Ya Fallasa Kansa. Hoto: @TheNationNews.
Asali: Twitter

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bayyana sun nuna cewa ya aikata laifin ne a tsakar dare a ranar 6 ga watan Satumban 2022 a Ikakumi Akoko.

Tope, wanda aka gurfanar a gaban alkalin kotun majistare a Akure kan tuhumar kisar gilla, ya nemi a masa afuwa.

Ba a san abin da ya kashe Stella ba har sai da danta ya yi magana

Mai gabatar da kara, Nelson Akintimehin, ya sanar da kotu cewa ba a san abin da ya yi sanadin mutuwar ta ba har sai da dan ya ce shi ya kashe ta.

Ya ce:

"Momoh a yayin da ya ke bayani ga yan uwansa ya ce dole ta sa ya shake mahaifiyarsa har sai da ta mutu saboda ta tada shi a tsakar dare tana zaginsa tana ta kiransa shege."

Akintimehin ya ce laifin ya saba da sashi na 319(1) na kudin masu laifi Cap 37, Vol. II ta dokar Jihar Ondo, 2006.

Kara karanta wannan

'A Soke EFCC,' Matasan Ibadan Suka Fada Wa FG, Sun Yi Babban Zanga-Zanga

Tope ya nemi sassauci

Da aka bukaci ya yi magana, Tope ya ce:

"Na kasa samun kwanciyar hankali a zuciya ta tun bayan da aka birne mahaifiyata. Hakan ya tilasta min fadin gaskiya cewa ni na shake ta ta mutu. Ina son kotu ta yi min sassauci."

Kotun ba ta amsa rokon Tope ba domin alkalin, Musa Al-Yunnus, ya bada umurnin a tsare shi a gidan gyaran hali na Olokuta.

Al-Yunnus ya daga cigaba da sauraron karar zuwa ranar 20 ga watan Oktoba.

Duniya kenan: Matashi mai shekaru 35 ya kashe mahaifiyarsa, ya gamu da fushin alkali

Wata kotun majistare da ke Ado Ekiti ta amince da bukatar da aka gabatar gabanta na ci gaba da tsare wani dan shekaru 35 mai suna Abiola Ayodeji a gidan gyara hali, Ado Ekiti.

Dan sanda mai gabatar da kara, Bankole Olasunkanmi ne ya bukaci hakan, domin ba rundunar yan sanda damar kammala bincike.

Kara karanta wannan

Son gaskiya: Soyayya ta sa wata kyakkyawar mata ta auri makaho, bidiyonsu ya ba da mamaki

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164