An Kama Fursunan Da Ya Tsere Daga Kuje Ya Yada Zango A Kano

An Kama Fursunan Da Ya Tsere Daga Kuje Ya Yada Zango A Kano

  • Abubakar Muhammad-Sadiq, wani fursuna da ya tsere yayin da yan bindiga suka farmaki magarkamar Kuje ya sake shiga hannu
  • Jami'an rundunar yan sandan Kano sun kama shi ne a unguwar Rangaza da ke karamar hukumar Ungogo na Jihar Kano
  • Abdullahi Kiyawa, Mai magana da yawun yan sandan Kano ya ce an mika wanda ake zargin a hannun hukumar kula da gidajen gyaran hali na Kano

Kano - Yan sanda a Jihar Kano sun kama wani da ake zargin yana daga cikin furunoni da suka tsere daga gidan yarin Kuje a unguwar Rangaza a karamar hukumar Ungogo, rahoton Premium Times.

Kakakin yan sandan Kano, Abdullahi Kiyawa, cikin sanarwar da ya fitar ya ce sunan wanda ake zargin, Abubakar Muhammad-Sadiq, 25, mazaunin Badarawa quaters, karamar hukumar Kaduna ta Arewa.

Kara karanta wannan

'Yan Sanda Sun Kai Samame Mafakar Masu Aikata Muggan Laifuka, Sun Samu Gagarumar Nasara a Katsina

Fursuna
An Kama Da Ya Tsere Daga Kuje A Kano. Hoto: @PremiumTimesNG.
Asali: Twitter

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Legit.ng ta rahoto yadda yan ta'adda suka yi amfani da abubuwa masu fashewa suka kutsa gidan yarin na Kuje a Abuja, hakan ya yi sanadin tserewar fursunoni fiye da 800 cikin 994.

An kamo da dama cikin wadanda suka tsere. Kuma, an halaka jami'in NSCDC da fursunoni hudu yayin harin.

Fursunoni
An Kama Fursunan Da Ya Tsere Daga Kuje Ya Yada Zango A . Hoto: @PremiumTimesNg.
Asali: Twitter

Abubakar Sadiq
An Kama Fursunan Da Ya Tsere Daga Kuje Ya Yada Zango A Kano. Hoto: @PremiumTimesNg.
Asali: Twitter

Mr Kiyawa ya ce an kama fursunan da ya tsere ne biyo bayan umurnin IGP, Alkali Usman, da kwamishinan yan sanda a Kano, Abubakar Lawal, na umurtar rundunar ta inganta tattara samo bayanan sirri da sa ido a unguwanni.

Yan sanda sun mika shi ga hukumar kula da gidan gyaran hali

Yan sandan sun ce an mika fursunan da aka kama a ranar 23 ga watan Satumba ga Hukumar kula da gidajen gyaran hali na Kano.

Kara karanta wannan

NNPC: Mun Gano Hanyar da Barayi Suka Yi Shekaru 9 Suna Satar Mai Ba a Ankara ba

Kakakin ya ce:

"Kwamishinan yan sanda yana godiya ga mutanen Kano saboda cigaba da bada hadin kai, goyon baya da tallafi.
"Ya yi kira ga mazauna jihar su cigaba da yi wa jihar da kasa addu'a kuma su rika kai rahoto ofishin yan sanda a maimakon daukan doka a hannu.
"Za a cigaba da bibiya bata gari a jihar a yayin da rundunar ke kokarin tabbatar da zaman lafiya a Jihar Kano. Don neman daukin gaggawa a kira; 08032419754, 08123821575 ko a yi amfani da manhajar "NPF Rescue Me" da za a iya sauke wa daga Playstore."

Harin gidan yarin Kuje: Yan sanda sun kama wani fursuna da ya tsere a jihar Ogun

A wani rahoto mai kaam da wannan, Rundunar yan sanda a Ogun a ranar Laraba, 13 ga watan Yuli, ta bayyana cewa ta kama wani da ya tsere daga gidan yarin Kuje, Yakubu Abdulmumuni, a yankin Sango-Ota da ke jihar.

Kara karanta wannan

ASUU Bata Da Wasu Dalilai Masu Kwari Na Ci Gaba Da Yajin Aiki - Buhari

Kakakin yan sandan jihar, Abimbola Oyeyemi, a cikin wata sanarwa da manema labarai a Ota, ya ce an kama wanda ake zargin ne a ranar Litinin, jaridar Premium Times ta rahoto.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164