'Yan IPOB Ba ’Yan Ta’adda Bane, Na Zauna da Su, Inji Peter Obi a 2017
- A wasu shekaru a baya, dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar Labour ya taba nuna damuwarsa ga yadda gwamnati ta haramta IPOB
- Gwamnatin Buhari na ci gaba da bayyana kyamarta da dukkan kungiyoyin aware a Najeriya saboda barazana da su suke ga kasar
- Ya zuwa yanzu, shugaban kungiyar IPOB na hannun gwamnati bisa zargin cin amanar kasa bayan kamo shi a kasar waje
Najeriya - Dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar Labour, Peter Obi ya taba kakabawa gwamnatin Najeriya laifi wajen ta'azzarar ayyukan barna daga 'yan awaren IPOB.
Ya kuma ga laifin gwamnati da ta ayyana kungiyar ta su Nnamdi Kanu a matsayin ta 'yan ta'adda, Premium Times ta ruwaito.
A ranar 1 ga watan Oktoban 2017 ne Peter Obi ya bayyana a gidan talabijin na Channels ya bayyana wadannan maganganu na ganin laifin gwamnati.
A wani bidiyon dake yawo a kafar YouTube, an ga lokacin da Peter Obi ke bayyana irin wadannan maganganu masu daukar hankali.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wacece kungiyar IPOB?
Kungiyar IPOB dai ba sabuwar kungiya bace, ta jima a Najeriya, inda take da'awa da babatun neman ballewa daga kasar.
Kungiyar ta sha kai hare-haren ta'addanci a yankin Kudu maso Gabas da ma wasu yankuna a Kudu maso Kudu a kasar nan, kuma takan ambata balo-balo cewa ita ta kai hare-haren.
Gwamnatin Najeriya ta haramta kungiyar a 2017, inda ta ayyanata a matsayin kungiyar 'yan ta'adda, haka nan Vanguard ta ruwaito.
Peter Obi kuwa, tsohon gwamna ne a jihar Anambra, ya kuma fada cewa gwamnatin Najeriya ta yi kuskuren ayyana IPOB a matsayin kungiyar 'yan ta'adda.
Ya bayyana balo-balo cewa, shi ya yiwa IPOB farin sani, kuma tabbas ba 'yan ta'adda bane domin ya zauna dasu.
Kotu Ta Wanke Tsohon Shugaban EFCC Magu Daga Zargin Sace Kudin Kasa
A wani labarin, wata kotun tarayya da ke zamanta a Abuja ta wanke tsohon shugaban hukumar EFCC, Ibrahim Magu daga zargin da ake masa na yin awon gaba da wasu kudade.
Mai shari'a Yusuf Halilu ne ya yanke hukuncin a jiya Talata 4 ga watan Oktoba, inda yace hujjojin da fasto Emmanuel Omale da matarsa suka gabatar na cewa Magu ya yi zambar N573m na cike kura-kurai.
Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa, ma'auratan biyu sun shigar da kara cewa, Magu ya umarce su da hada baki wajen sace kudade masu yawa.
Asali: Legit.ng