Gwamnatin Zamfara Ta Zata Fara Biyan Ma'aikata Mafi Karancin Albashi N30,000
- Gwamnatin Zamfara ta amince da fara aiwatar da mafi karancin Albashi ga ma'aikatan jihar a watan Nuwamba
- A wata sanarwa daga ofishin mataimakin gwamna, Sanata Hassan Nasiha, gwamnatin ta yaba wa ƙungiyoyin kwadugo na jihar
- Sanata Nasiha ya jinjina wa wakilan gwamnati bisa cimma matsaya kan batun ƙarin Albashin
Zamfara - Gwamnatin jihar Zamfara ƙarƙashin jagorancin gwamna Bello Matawalle ta amince a gaggauta aiwatar da tsarin mafi ƙarancin albashi N30,000 ga ma'aikatan jihar.
Wannan na ƙunshe ne a wata sanarwa da Babangida Umar, darakta Janar na harkokin yaɗa labarai a ofishin mataimakin gwamna ya fitar yau Laraba a Gusau, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Mataimakin gwamna, Sanata Hassan Nasiha, ya bayyana haka ne lokacin da ya karbi yarjejeniya da kwafin kunshin fahimtar juna (MoU) mai ɗauki da sa hannun tsagin gwamnati da kungiyoyin kwadugo.
Sanata Nasiha ya nuna gamsuwarsa bisa yadda ƙungiyoyin kwadugo suka nuna wayewa da fahimta yayin tattauna wa da wakilan gwamnatin jiha kan batun.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
A ruwayar Premium Times, Mataimakin gwamnan yace:
"Fahimtar da suka nuna ta haifar da cimma matsayar fara biyan mafi ƙarancin Albashi na N30,000 a watan Nuwamba."
"Halin matsin tattalin arziƙi da ake fama da shi a yanzu da ƙalubalen tsaro na daga cikin abubuwan da gwamnati ta yi la'akari da su kafin amince wa da fara biyan mafi ƙarancin Albashi."
Bugu da ƙari ya yaba wa kwamitin wakilan gwamnati karkashin jagorancin Ambasada Bashir Yuguda bisa namijin kokarinsu na samun matsaya ɗaya da ƙungiyoyin.
NLC ta gode wa gwamnatin Matawalle
Ƙungiyoyin kwadugo, bisa wakilcin shugaban ƙungiyar NLC na jiha, Sani Halilu, sun gode wa gwamnatin Matawalle bisa amince wa da tsarin mafi ƙarancin Albashi ga ma'aikata.
Idan Nayi Nasara Zan Sake Fasalin Najeriya Tare Habaka Tattalin Arziki Kasar, Kwankwaso Ya Yi Alkawari
Ya kuma yaba wa ma'aikatan jihar Zamfara bisa goyon bayan da suka bai wa ƙungiyoyin kwadugo lokacin da suke fafutukar neman ƙarin albashi.
A wani labarin kuma Kakakin majalisar wakilai ya bayyana abinda suka tattauna da shugaba Buhari kan yajin aikin ASUU
A ranar Talata, shugabannin majalisar dokokin tarayya suka gana da shugaba Buhari kan yajin aikin ƙungiyar Malaman jami'o'i.
Kakakin majalisar, Femi Gbajabiamila, ya bayyana cewa taron ya yi armashi kuma zasu sake koma wa ranar Alhamis.
Asali: Legit.ng