‘Yan Majalisa Sun Fara Aikin Ruguzawa da Dunkule Ma’aikatu Domin Rage Kashe Kudi
- Kwamitin majalisar tarayya ya yi zaman farko a shirin gano MDA da ake ganin ba su da amfani a Najeriya
- Hon. Victor Danzaria ya jagoranci ‘yan majalisa domin ayi bincike a kan hukumomin da ba a bukata
- Akwai cibiyoyi, hukumomi da ma’aikatun gwamnati wanda ake tunanin za a soke su domin rage batar da kudi
Abuja – Mun ji ‘Yan majalisar wakilan tarayya sun soma aiki domin a soke ko a dunkule wasu ma’aikatu, hukumomi da cibiyoyin gwamnatin tarayya.
Punch tace kwamiti na musamman da aka kafa a majalisa domin gano ma’aikatu da hukumomin da suke mai-mai wajen aikinsu sun soma wannan shiri.
Majalisar wakilan kasar za tayi wannan ne da nufin kudin da ake kashewa duk shekara ya ragu. Har ila yau wannan zai gyara aikin ma’aikatan tarayya.
Kwamitin da aka ba wannan aiki na musamman ya bukaci hukumomin gwamnati da abin ya shafa suyi kokarin gamsar da su ana bukatar aikin da suke yi.
An soma yin zama a Abuja
A zaman farko da kwamitin ya yi jiya a Abuja, sun zauna da hukumomi uku masu kama da juna.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Wannan kwamiti ya gayyaci hukumar da ke kula da gidajen tarihi da kuma hukumar kula da al’adu da fasaha da hukumar nan mai kula da harkar shakatawa.
Shugaban kwamitin, Honarabul Victor Danzaria a jawabin da ya gabatar a kafin a fara zaman, yace aikin kwamitinsa shi ne a duba MDA da za a ruguza.
Kwamitin yana da nauyin gano hukumomi da ma’aikatun da ya dace a soke ko a hada su, sai ya ba gwamnatin tarayya shawarar abin da ya kamata.
Kokarin da muke yi - DG NCAC
Shugaban hukumar NCAC, Otunba Segun Runsewe ya shaidawa ‘yan kwamitin a kokarinsu, sun yi yunkuri wajen takawa shirin Big Brother Nigeria burki.
Otunba Segun Runsewe ya kuma ce sun yi maganin Idris Okuneye wanda aka fi sani da Bobrisky.
Hon. Alex Egbonna ya ankarar da Darekta Janar din na NCAC cewa har yanzu ana nuna tsiraici a shirin BBN duk da kokarin da yake ikirarin hukumarsa tayi.
Magana tayi nisa - Sanata
Kwanaki aka samu rahoto shugaban kwamitin tattalin arziki a majalisar dattawa, Sanata Olamilekan Adeola yace akwai maganar soke ma’aikatun gwamnati.
Sanata Olamilekan Adeola yake cewa za a iya yin wannan aiki ne a shekara mai zuwa kamar yadda kwamitin Stephen Orosanyeya ya ba gwamnati shawara.
Asali: Legit.ng