FG Ta Bude Kafar Cike Tallafin Kudi N75,000 Ga Dalibai a Kowane Zango
- Gwamnatin Najeriya ta fara ba daliban manyan makarantun sama da sakandare a Najeriya kudin makaranta
- Ministan ilmi na kasar, Adamu Adamu ya bayyana cewa wannan kudin karatu za a fara ba da shi ne ga wasu sashen daliban da ke karatu a jami'o'in gwamnati
- Gwamnati za ta ba daliban jami'o'in gwamnati N75,000 a kowane zango da kuma N50,000 ga daliban da ke karatu a kwalejin ilimin gwamnati
FCT, Abuja - Gwamnatin Najeriya ta bayyana cewa, ta bude kafar yanar gizon da dalibai za su cike fom din tallafin kudi da za a basu.
Ministan ilimi, Mallam Adamu Adamu ya bayyana cewa, shugaba Buhari ya amince ake ba wasu daga daliban jami'o'in gwamnati da na kwalejin ilimin gwamnati kudin rage radadin karatu.
Adamu ya ce, daliban jami'a da ke karanta fannin koyarwa za su samu N75,000 duk zango yayin da daliban kwalejin ilimi kuwa za su fara samun N50,000 duk zangon karatu.
An cika alkawari
A bikin murnar ranar malaman makaranta ta duniya da aka yi a Abuja a 2021, Adamu ya bayyana cewa, yana daga manufar gwamnatin Buhari ingantawa tare sake dawo da martabar aikin koyarwa.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Wannan yasa gwamnati ta yanke shawarar fara ba da kudi ga masu karanta fannin koyarwa don karfafa musu gwiwa.
Adamu yace:
“Daliban digirin B.Ed/B.A. Ed/BSc. Ed a jami'o'in gwamnati za su fara karbar N75,000 duk a zangon karatu yayin masu yin NCE kuma za su fara samun N50,000 na kudi a kowane zangon karatu"
Wani rahoton BusinessDay ya bayyana hanyar dalibai za su bi don iya samun damar cin wannan gajiya ta gwamnati.
Gwamnati ta ce dole dalibi ya zama yana karatu ne cibiyar ilimi ta gwamnati kuma yana karatun ba na wucin gadi ba.
Abubuwan da ake bukata
Dukkan daliban da ke sha'awar cin wannan kudi, ciki har da nakasassu, dole su kasance a ajin farko ko fiye da hakan.
Hakazalika, wadanda ke morar wani tallafin karatu ba za su samu wannan sabon tallafi ba. Ana bukatar dalbi ya cike fom ta yanar gizo, ya buga shaidar cike fom din sannan ya kai kwafin takardar ma'aikatar ilimi.
Wannan batu dai na zuwa ne a daidai lokacin da jami'on Najeriya ke garkame bisa yajin aikin da kungiyar malamai ta ASUU ke yi.
Ku Janye Yajin Aikin Nan Don ’Ya’yanmu Mu, Kakakin Majalisa Ya Roki ASUU
A wani labarin kuma, Femi Gbajabiamila, kakakin majalisar wakilai a Najeriya ya yi kira ga kungiyar malaman jami'o'i ta ASUU da su duba tare da janye yajin aiki saboda biyan muradan dalibai a kasar.
Ya bayyana hakan ne yayin dagawa da ASUU, ministan kwadago Chris Ngige da mukaddashin akanta janar na kasa Okolieaboh Sylva a jiya Alhamis 29 ga watan Satumba.
A cewarsa:
"Ba zai yiwu a ce kowa ya yi kuskure ba. Muna tafiya kan abin da muka ce a zamanmu na karshe, don Allah saboda muradin 'ya'yanmu, muna rokonku ba wai don umarnin kotu ba."
Asali: Legit.ng