Masana Sun Gargadi 'Yan Najeriya Kan Cin Mushe, Sun Jero Illar da Ka Iya Shafar Mutum
Masana a fannin lafiya sun gargaɗi 'yan Najeriya su guji cin naman dabbobin da suka mutu kafin sarrafa su yadda ya kamata, a cewarsu cin irin waɗan nan dabbobi ka iya jefa mutum cikin mawuyacin halin rashin lafiya.
Masanan sun jaddada cewa cin naman matattun dabbobi ka iya jawo mutane su kamu da cututtuka, waɗanda ke yaɗuwa daga dabbobi zuwa jikin mutane, kamar yadda Punch ta ruwaito.
Haka zalika masanan lafiyan sun roƙi 'yan Najeriya su kula sosai da wuraren da suke sayen naman dabbobin da suke ci, inda suka ce za'a iya sayar wa kwastomomi masu yarda matattun dabbobi.
Bugu da ƙari, sun bayyana cewa za'a iya samun naman mushe a gidajen abinci, bisa haka suka ƙara gargaɗi da babban murya cewa mutane su kula da wuraren da suke sayen abinci.
A bayanin kwararrun lafiya, girki ba zai iya lalata gubar da ke jikin naman mushen dabbobi ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Da suke zantawa da jaridar, wasu kwararru a fannin lafiya, Farfesa a Kwas din Public Health, Tanimola Akande, da wani kwararren likitan dabbobi, Chidozie George, yace ba wai don haramcin addini ake gargaɗin mutane su guji naman mushe ba.
Illolin cin naman mushe ga mutane
A cewarsu, ana gargaɗin 'yan Najeriya su guji naman mushe ne saboda kula da lafiyarsu da kuma sakamakon da cin naman ka iya haifarwa ga lafiyarsu.
Farfesa Akande yace idan dabba ta mutu, komai zai tsaya cak ya daina aiki, sassan jiki irinsu Zuciya, Kunhu da sauransu zasu tsaya cak.
Hakan a cewar Farfesan zai ƙara yawan kwayoyin cututtuka ba tare da samun tirjiya ba, ya ƙara da cewa waɗannan kwayoyin ka iya sauya wa zuwa guba.
"Irin haka ke aukuwa idan ba'a gaggauta sanya dabbar a cikin Firji ko aka dafa ba bayan ta mutu," inji shi.
Ya bayyana cewa wasu dabbobin na mutuwa ne sakamkon cutar da ta kama su kamar Tarin Fuka kuma suna iya shiga jikin mutum idan ya ci naman. Wasu cututtukan ka iya shafar mutum ta wannan hanyar a cewarsa.
"Wasu dabbobin sun mutu ne sakamakon cuta, idan aka ci namansu mutum ka iya kamuwa da cutar da suke fama da ita," a gargaɗinsa.
Gashi ko dafa nama baya kashe cutar jikin mushe - Masani
A jawabinsa, kwararren likitan dabbobi, Dakta Chidozie George, yace ko da an gasa irin wannan naman, cutar da ta yi sanadin mutuwar dabbar ba zata gushe ba, haka zalika dafa naman ba zai gusar da cutar ba.
Ya gargaɗi masu gidajen gona su guji sayar wa mutane da matattun dabbobi. Yace, "Suna ganin hakan wata hanya ce ta samun kudi, suna sayar wa mutane musamman tsintsaye."
"Duba da asalina da ilimina, ba na yarda na ci naman kazar da bansan lokacin da aka yanka ta ba. Bana cin naman duk wada kazar da ba'a gabana aka ƙasheta ba."
A wani labarin kuma Zakuna Sun Yi Kaca-Kaca da Wasu ’Yan Ta’adda da Sunan Jihadi a Mozambique
Bernardino Rafael, kwamandan 'yan sanda a kasar ne ya bayya hakan, inda yace mutane 16 da suka mutu sun mutu ne sakadamakon arangama da sojoji.
A wani yanayi mai ban mamaki, ya kuma ce zakuna da kadajoji ne suka afka ma wasu daga cikin 'yan ta'adda.
Asali: Legit.ng