2023: An Bayyanawa 'Yan Siyasa Muhimman Wurare 3 da Zasu Kauracewa Yayin Kamfen

2023: An Bayyanawa 'Yan Siyasa Muhimman Wurare 3 da Zasu Kauracewa Yayin Kamfen

  • Lauya masanin kundin tsarin mulkin Najeriya, Kayode Ajulo, ya gargadi 'yan siyasa da jam'iyya da su yi biyayya ga sabbin dokokin zaben Najeriya
  • Ya tunatar da cewa, dokokin sun haramta kamfen din siyasa a fadar sarakunan gargajiya, Masallata da Majami'u a kasar nan
  • Ya bayyana cewa, fadar sarakunan gargajiya duk da kjudin al'umma aka gina su kuma da shi ake kula da su, don haka ofisoshin gwamnati ne

FCT, Abuja - Wani Lauya masanin tsarin mulki, Kayode Ajulo, ya gargadi ‘yan siyasar Najeriya da jam’iyyun siyasa da su gujewa rashin biyayya ga tanade-tanaden dokar zabe ta 2022, musamman dangane da gudanar da kamfen gabanin babban zabe na 2023.

Kamfen din Zabe
2023: An Bayyanawa 'Yan Siyasa Muhimman Wurare 3 da Zasu Kauracewa Yayin Kamfen. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Ajulo ya tunatar da ‘yan takarar da ke neman mukamai daban-daban a zabe da ke tafe da cewa bisa ga tanadin dokar zabe, an sanya takunkumi da yawa don hana magudin zabe da aka saba farawa ko da lokacin kamfen.

Kara karanta wannan

Dole ku zo nan: ‘Yan Majalisar Najeriya Sun Bukaci Hameed Ali Su Bayyana Gabansu

Lauyan a wata hira da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya, NAN, a ranar Laraba a Abuja, ya bukaci ’yan siyasa, jam’iyyu da sauran kungiyoyin kamfen da su gujewa yin kamfen a fadar sarakunan gargajiya a dukkan fadin kasar nan.

Ya ce, fada wuraren da aka gina kuma ake kula da su ne da kudin jama’a, kuma bai kamata a yi amfani da su a matsayin filin wurin kamfen ba, ya kara da cewa irin wannan taka dokar dokar zabe zai haifar da sakamako maras kyau.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Lauyan masanin kundin tsarin mulki, yayin da yake yanko sashin da ya dace ya ce:

"Sashe na 92 ​​na dokar zabe, 2022, ya tanadi haramcin zuwa wasu wurare a yakin neman zabe."

Wannan, in ji shi ya hada da wani tanadi na dole cewa yakin neman zabe ko taken siyasa ba za a gurbata shi da kalaman batanci kai tsaye ko a fakaice ba da zai iya cutar da addini, kabilanci, ko bangaranci ba.

Kara karanta wannan

Gwamnoni 4 na Najeriya da Nijar Sun yi Muhimmiyar Ganawa a Maradi

A cewarsa, ba za a yi amfani da kalaman batanci, rashin mutunci, son zuciya, zage-zage ko wasu kalamai da aka tsara ko masu yuwuwa su haifar da tashin hankali a yakin neman zabe ba.

Ya ce ba za a yi amfani da wuraren da aka killace don ibadar addini, ofisoshin ‘yan sanda da ofisoshin gwamnati ba wajen kamfen zabe.

Sauran sun hada da kamfen da jerin gwano; yadawa, ko kai hari ga jam'iyyun siyasa, 'yan takara ko shirye-shirye ko akidun su.

“Ta hanyar wannan dokokin na sama wanda ya haramta amfani da ofisoshin gwamnati wajen kamfen, yana da kyau mu sanar cewa fadar sarakunan mu da ake kula dasu da dukiyar jama’a an karkasa su a matsayin ofisoshin gwamnati.”

Daily Trust ta rahoto cewa, shugaba Muhammadu Buhari ya sanya hannu kan sabuwar dokar zabe ta 2022, a ranar 25 ga watan Fabrairu, inda ta soke dokar zabe ta 2010.

Kara karanta wannan

2023: Matsaloli 5 da ke faruwa duk lokacin da aka fara kamfen a Najeriya

Sashi na 92, 93, 94, 95 da 96 na sabbbin dokokin zabe sun yi hani tare da hukunci ga kamfen din zabe a wuraren ibada, fadoji, da wuraren da ke da ofisoshin gwamnati.

Hakazalika akwai sakamakon tursasawa, sayen kuri’u, magudi, jabun katin zabe, kwace akwatin zabe da sauran kura-kuran zabe.

An Gano Yadda Tinubu Ya Assasa Rikicin APC kan Kwamitin Yakin Neman Zabensa

A wani labari na daban, manyan alamu na nuna cewa mai 'dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Bola Tinubu, ya shuka sabuwar rigima a kwamitin yakin neman zabensa na shugaban kasa (PCC) bayan ya zagaye shugaban kasa Muhammadu Buhari, shugabancin jam'iyya da gwamnonin jam'iyyar wurin kafa kwamitin.

Jaridar Thisday ta rahoto cewa, sassa uku ne aka tsara wanda ya hada da 'dan takarar shugaban kasa, jam'iyya da shugaban kasa wadanda zasu samu jagorancin gwamnoni tunda su ne zasu jagoranci yakn nemen zaben a jihohinsu.

Kara karanta wannan

An kama fasto a jihar Arewa bisa bude asibiti a cocinsa, yana ba da maganin bindiga

Asali: Legit.ng

Online view pixel