Rikicin Makiyaya: Abin na ci mani tuwo a kwarya - Buhari
- A yau Shugaba Buhari yayi magana kan rikicin Makiyaya
- Shugaba Buhari yace kwanan nan za a ga karshen rikicin
- Shugaban kasar yace ya sa Jami’an tsaro su dage da aiki
Mun samu rahoto cewa Shugaban Kasa Muhammmadu Buhari ya sha alwashin kawo karshen kashe-kashe da sauran rikicin da ake fama da shi tsakanin Makiyaya da sauran Jama’a a fadin kasar nan.
Shugaba Buhari ya bayyana cewa zai kawo karshen rikicin Makiyayan ne a yau Litnin a fadar Shugaban kasar lokacin da ya gana da wasu manyan Darektoci na kasar ta bakin mai magana da yawun sa watau Mista Femi Adesina.
KU KARANTA: Wanda ake sa ran zai yi takara da Shugaba Buhari ya gamu da cikas
Rikicin da ya ki ci ya kuma ki cinyewa ya addabi ‘Yan Najeriya inda aka yi asarar dukiya da rayuka da dama. Shugaban kasar yace wannan ta’adi da ake yi a kasar yana sosa masa zuciya kuma abin da ya dame sa kwarai da gaske.
Shugaban ya bayyana cewa tuni ya sa Jami’an tsaro su bazama aiki wajen ganin an kawo karshen ta’asar da wasu Makiyaya ke yi. Yanzu haka da mu ke magana an aika rundunar inda ake gudun barkewar wannan barna a fadin Najeriya.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng