Ta Tabbata, Hotunan Yadda Makarantun Sakandaren Bauchi Suka Fara Raba Maza da Mata a Aji

Ta Tabbata, Hotunan Yadda Makarantun Sakandaren Bauchi Suka Fara Raba Maza da Mata a Aji

  • Kwamishinan ilimin jihar Bauchi ya fitar da sanarwar da ke bayyana yadda aka yi zaman aji a jihar bayan raba daliban sakandare - maza da mata
  • Gwamnatin jihar Bauchi ta raba daliban sakandare a ajujuwa saboda wasu dalilai da tace tana son cimmawa
  • Dalibai a jihar Bauchi sun yi zanga-zanga kan matakin gwamnatin jihar Bauchi na raba maza da mata a aji daya

Jihar Bauchi - Kwamishinan ilimi na jihar Bauchi, Dr. Aliyu U. Tilde ya yada hotunan yadda makarantun sakandaren jihar Bauchi suka kasance a yau Laraba 28 ga watan Satumba bayan raba dalibai maza da mata a aji.

Gwamnatin jihar Bauchi ta sanya sabuwar dokar da ta raba tsakanin dalibai maza da mata a jihar, lamarin da ya jawo cece-kuce, har dalibai suka yi zanga-zanga a jihar.

Kara karanta wannan

Tsagerun Yan Bindiga Sun Kashe Sojoji 5 Da Dan Farar Hula Daya A Anambra

Yadda ajujuwan dalibai suka kasance a Bauchi
Ta Tabbata, Hotunan Yadda Makarantun Sakandaren Bauchi Suka Fara Rana Maza da Mata a Aji | Hoto: Aliyu U. Tilde
Asali: UGC

A hotunan da Dr Tilde ya yada na makarantun sakandaren a yankunan jihar daban-daban, ya bayyana godiyarsa ga Allah bisa tabbatar wannan lamari, inda yace:

"Mun gode wa Allah da ya karbi addu’o’inmu na fara tsarin makarantun sakandare na mata-zalla kamar yanda aka tsara a Jaharmu ta Bauchi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Ranar litinin da ta wuce, ilahirin makarantun da aka fara da su a garuruwa dabam dabam a jahar sun bude kuma y’an makaranta sun je makarantunsu."

Wannan somin-tabi ne, zamu saurari koke daga iyayen dalibai

A bangare guda, ya bayyana cewa, a tsawon mako guda za a saurari iyaye da dalibai da masu ruwa tsaki don aika koke-kokensu.

Hakazalika, ya ce ma'aikatar ilimi za ta saurari batun iyaye ne da ya shafi inda aka tura 'ya'yansu da kuma gano wadanda ba a tura wasu makarantun ba.

A kamalansa:

Kara karanta wannan

An Yi Arangama Tsakanin Yan Sanda Da Yan Kalare A Gombe, Wasu Sun Jikkata

"Za mu yi amfani da wannan satin a matsayin gwaji da karban koke koke daga iyaye da dalibai a bisa makarantun da aka tura su ko rashin fitar sunayensu a jadawalin tura daliban. Daidai sai Allah."

An tunzura dalibai sun yi zanga-zanga a Bauchi

Hakazalika, kwamishinan ya ce an samu tsaiko tare da tunzura wasu dalibai da yawansu bai taka kara ya karya ba a jihar, inda aka tunzura su suka fito zanga-zanga.

Ya kara da cewa:

"Mun lura da yamadidi da karin gishiri wanda wadanda ba sa son shirin suka rika yi don wasu yara kamar 50 daga makarantu biyu a garin Bauchi (GDSS na Kofar Idi da Kofar Wambai) sun yi zanga zanga ran Litinin kan tura su GCDSS Bauchi.
"Da ma duk tsari mai kyau ba ya rasa kalubale ko me kashinsa. Mutanen gari sun shirya fitowarsu jiya amma shiru kake ji, wai ruwa ya ci makadi."

Kara karanta wannan

Akeredolu: Babu Gudu Babu ja da Baya kan Shirin Ba Sojojin Amotekun Makamai

Bauchi: Raba Mata Da Maza A Makarantun Sakandare Ya Harzuka Dalibai, Sun Mamaye Tituna Suna Zanga-Zanga

A wani labarin, daliban makarantun sakandare a halin yanzu suna zanga-zanga a titunan Bauchi kan wata sabuwar doka da gwamnati ta kawo na raba mata da maza a makarantu.

Dalibai sun koma makaranta ne a hukumance yau (Litinin) a sassan jihar kamar yadda jaridar Vanguard ta rahoto.

Kwamishinan Ilimi na Jihar Bauchi, Mr Aliyu Tilde, ya ce gwamnatin jihar ta kammala shiri don raba dalibai mata da maza a makarantun jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.