Yadda DSS Ta Cafke Soja 'Mai Sayar Wa Masu Garkuwa Bindigu' A Abuja
- Jami'an hukumar DSS tare da yan bijilante sun kama wani soja da ke sayarwa da bada hayar bindiga ga masu garkuwa
- An shirya masa tarko ne aka ce ya kawo wani bindiga kirar AK47 za a siya a hannunsu amma da ya kawo sai jami'an tsaro suka kama shi
- Wasu masu garkuwa da ke hannun DSS ne suka tona masa asiri inda suka ce ya basu hayar bindiga a baya sun kuma biya shi kasonsa daga kudin fansa
Abuja - Jami'an yan sandan farin kaya DSS sun kama wan soja da ke aiki da Muhammadu Buhari Cantonment in Tungan-Maje a Abuja kan bada haya da sayar da bindiga ga masu garkuwa da mutane, Daily Trust ta rahoto.
City & Crime ta gano cewa an kama shi ne sakamakon wani atisaye da aka yi a makon da ta gabata a kusa da Tashar Dankogi a Zuba da hadin gwiwan kungiyar yan bijilante a yankin.
Majiya ta shaidawa City & Crime cewa DSS daga Gwagwalada sun nemi taimakon kungiyar tsaron na unguwar a Zuba don kama wanda ake zargin bisa zargin da aka taba masa a baya na dillancin bindigu.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Majiyar ta ce:
"An gano cewa wanda ake zargi, a farko, ya bada hayar bindigarsa don a yi garkuwa da mutane kan kudi N300,000.
"Sai a karo na biyu, an tuntube shi kan wani garkuwar kuma ya nemi a biya shi N200,000 wanda aka ce masu garkuwan sun biya amma ya gaza ba su bindigan."
Yadda aka shirya wa sojan tarko kuma ta kama shi - Majiya
Majiyar ta ce a lokacin da masu garkuwa da ke hannun DSS suka yi wa sojan wannan zargin, sai aka shirya masa tarko.
"Sai aka tuntube shi da wata kwangilar aka ce ya kawo musu bindigu AK47 da za su siya kan kudi Naira miliyan 3.
"Muka tafi wurin da aka shirya haduwar a nan Zuba muka boye. Ya iso wurin da motarsa don mika bindigan, lokacin muka fito muka kama shi da bindigar a nade."
Majiyar ta sanar da wakilin majiyar Legit.ng cewa an gano wani AK47 din da harsashi 30 a wani sako a motarsa.
Majiyar ta kara da cewa:
"Mun tafi da shi ofishin mu inda aka rattaba hannu kan takarda da DSS sunnan muka mika musu shi."
An gano cewa jami'an sojoji daga hedkwata daga Abuja sun gana da yan bijilante a ofishinsu a Zuba bayan kwana daya da kama shi inda suka nemi bayyanin yadda aka kama shi.
Masu Garkuwa Sun Fada Komar Yan Sanda Yayin Da Suke Kokarin Karbar Cikon Kudin Fansa A Wata Jihar Arewa
A wani rahoton, rundunar yan sandan Jihar Gombe a ranar Talata ta yi holen wani Mohammed Aminu da Salisu Sa'idu, wadanda aka kama yayin karban kudin fansa N300,000 daga iyalan wadanda suka sace.
A cewar kakakin rundunar, Mahid Abubakar, hakan na zuwa ne bayan tawagar masu garkuwar sun karbi N100,000 bayan sace wani Jibrin Muhammad a Jihar Taraba, rahoton The Punch.
Asali: Legit.ng