Kotu Ta Daure Basaraken Gargajiya a Legas Tsawon Shekaru 15 a Gidan Yari

Kotu Ta Daure Basaraken Gargajiya a Legas Tsawon Shekaru 15 a Gidan Yari

  • Wata kotu a jihar Legas ta daure wani basarake bisa kama shi da laifukan ta'addanci guda biyu, kuma hannu dumu-dumu
  • Hakazalika, kotu ta daure kanin barasaken, Opeyemi Mohammed, duk za su shafe shekaru 15 a magarkama
  • A baya hukumomin jihar Legas sun tsige barasaken bayan gano ya yi karyar an yi garkuwa dash

Jihar Legas - Wata babban kotun da ke zama a Ikeja ta daure wani basaraken da aka tsige, Bale na Shangisha a Mogodo, Mutiu Ogundare, inda zai zauna a magarkama na shekaru 15, The Nation ta ruwaito.

An kama shi da laifin karyar cewa wasu sun yi garkuwa dashi, lamarin da ya sa kotu ta tasa keyarsa zuwa gidan gyaran hali.

Yadda kotu ta daure basaraken da ya yi karyar an yi garkuwa dashi
Kotu Ta Daure Basaraken Gargajiya a Legas Tsawon Shekaru 15 a Gidan Yari | Hoto: dailypost.ng
Asali: UGC

Mai shari'a Hakeem Oshidi ya yankewa Ogundare hukunci ne bayan kama shi da laifuka biyu na tada hankalin jama'a da kuma karyar cewa an yi awon gaba dashi.

Kara karanta wannan

Yanzu-yanzu: Wutar Lantarki Ta Dauke A Najeriya Gaba Daya Da Safiyar Nan, 0 Megawatt

Hakazalika, kotun ta kuma daure dan uwansa, Opeyemi Mohammed na tsawon shekaru 15 kamar yadda aka yankewa basaraken.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Sai dai, kotun ta ba da umarnin a saki matarsa, Abolanle bayan wanke ta daga dukkan zargin da ake mata.

A baya, tsohon gwamnan jihar Legas, Akinwunmi Ambode ya dakatar da basaraken bayan gani laifin da ya aikata, rahoton Daily Post.

Bayan shekaru biyar da dakatar dashi ne kotu ta yanke hukunci, ta tasa keyarsa zuwa gidan yari tare da kaninsa.

Jihohin Najeriya na fuskantar barazanar garkuwa da mutane, gwamnati ta ce tana iya kokarinta wajen ganin ta shawo kan matsalolin tsaro.

'Yan Najeriya na ci gaba da koka yadda lamurran tsraon kasar ke kara dagulewa.

Sojin Sama Sun Sake Ruwan Bama-Bamai Kan Maboyar ’Yan Bindiga a Zamfara

A wani labarin na daban kuma, rahoton da muke samu ya bayyana cewa, rundunar sojin saman Najeriya ta sake gano mafakar 'yan ta'adda karkashin jagorancin Dan Karami a karamar hukumar Zurmi ta jihar Zamfara.

Kara karanta wannan

Tashin hankali yayin da yaro karami ya nutse a tafki a wata jihar Arewa

Jaridar Punch ta ce, sojojin sun yi nasarar jefa bama-bamai kan mafakar 'yan bindigan da ke addabar jama'ar yankin.

A cewar wata majiyoyi daga yankin, an kashe wasu 'yan bindiga da dama a harin da aka kai jiya Alhamis 22 ga watan Satumba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.