Yan Bindiga Sun Kashe Dan Sanda Da Wasu 3, Sun Yi Awon Gaba Da Mutane Masu Yawan Gaske A Jihohin Arewa 2

Yan Bindiga Sun Kashe Dan Sanda Da Wasu 3, Sun Yi Awon Gaba Da Mutane Masu Yawan Gaske A Jihohin Arewa 2

  • Yan bindiga da ake zaton masu garkuwa da mutane sun sun kai munanan hare-hare jihohin Katsina da Kaduna
  • A Kaduna maharan sun kashe mutane uku sannan suka yi awon gaba da wasu mutum 22 a garuruwan Birnin Gwari
  • Yan bindigar sun kuma halaka wani jami'in dan sanda wanda yayi kokarin dakile wani hari a hanyar babban titin Katsina-Jibia da ke jihar Katsina

Tsagerun yan bindiga sun bindige wasu mutane uku sannan suka yi awon gaba da wasu 22 yayin da suka farmaki garuruwan Birnin Gwari da ke jihar Kaduna, Daily Trust ta rahoto.

Harin ya wakana ne a ranar Asabar da misalin karfe 7:30 na yamma lokacin da maharani suna mamaye Hayin Gada na garin Damari da ke gudunmar Kazage, inda suka kashe mutum biyu Sanusi Zubairu da Kabiru Zubairu.

Kara karanta wannan

Kaduna: 'Yan Bindiga Sun Sheke Manoma 3, Sun yi Garkuwa da Wasu 22

Sun kuma sace mutane 12 sannan suka yi sace-sace a shagunan wannan garin.

Yan bindiga
Yan Bindiga Sun Kashe Sufeton Dan Sanda Da Wasu 3, Sun Sace Mutane Masu Yawan Gaske A Jihohin Arewa 2 Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Shugaban kungiyar BEPU, Ishaq Usman Kasai, wanda ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya saki a ranar Litinin, ya ce a wannan ranar maharan sun kashe mutum daya sannan suka yi awon gaba da mutum shida a wani gona da ke hanyar Birnin-Gwari/Kaduna.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ya ce yan bindigar sun kuma yi garkuwa da wasu mutum hudu a Dajin Jangali sannan suka kwace Babura uku daga manoma a yankin Kamfanin Doka.

Kasai ya nuna damuwa cewa yan bindigar na ci gaba da farmakar garuruwa daban-daban da yin sace-sace ba tare da tangarda ba.

Da aka tuntube shi, kakakin yan sandan jihar, DSP Jalige Mohammed, ya yi alkawarin samo Karin bayani daga yankin kafin yace komai.

Mahara sun kuma farmaki al'ummar Katsina

Kara karanta wannan

Zamfara: 'Yan Bindiga Sun Kai Sabon Kazamin Hari Kan Bayin Allah, Sun Kashe Rayuka

Channels Tv ta kuma rahoto yan bindiga a ranar Litinin sun kashe wani sufeton dan sanda, Idris Musa, sannan suka cinnawa abar hawarsa wuta a hanyar babban titin Katsina-Jibia da ke jihar Katsina.

An kuma ce sun sace matafiya da dama a yayin faruwar lamarin wanda ya gudana a garin Makera, yan kilomita kadan daga birnin Katsina.

Wani ganau ya bayyana cewa yan ta’addan sun toshe hanya da misalin karfe 8:00 na safe, suna ta harbi don tsayar da wani bas da ke dauke da fasinjoji zuwa garin Katsina.

Kakakin yan sandan jihar, SP Gambo Isah, ya tabbatar da lamarin ga manema labarai, inda yace marigayin dan sandan yayi kokarin dakile harin yan ta’addan amma bai cimma nasara ba sai maharan suna farmake shi inda suka harbe shi har lahira.

Ya yi bayanin cewa yan ta’addan sun kona abar hawan marigayin kafin suka sace wasu fasinjoji da ba a san adadinsu ba zuwa jeji.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Yan Ta'adda Sun Sake Kai Hari Masallacin Juma'a a Zamfara, Sun Kashe Masallata Da Yawa

Ya ce:

“Sun kashe shi a nan take sannan suka sace fasinjoji da dama wadanda suka hau wasu motocin kasuwa daga karamar hukumar Jibia zuwa garin Katsina don gudanar da harkokinsu.”

'Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Wani Sarki Mai Martaba A Jihar Filato

A wani labarin, wasu tsagerun 'Yan bindiga a farkon awannin Litinin (yau) sun yi awon gaba da Sarkin gargajiya na masarautar Tal da ke ƙaramar hukumar Pankshin a jihar Filato, Alhaji Dabo Gutus.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa basaraken da ya shiga hannun 'yan ta'adda shi ke rike da Sarautar da ake kira, "Ngolong Tal" (Sarki mai daraja ta uku). An ce sun sace shi da misalin ƙarfe 1:00 na dare.

Wani mazaunin yankin Masarautar yace mutane na ƙoƙarin tuntuɓar masu garkuwa da mutanen domin jin menene asalin matsalar da ta kai ga sace sarkinsu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng